Wani mazauni a yankin Uruagu, mai suna, Peter Orji, ya kashe yayansa saboda zargin da ake yi wa Peter na kin biyan kudin wutar Lantarki da ya yi amfani da ita.
An ruwaito cewa, Peter ya hallaka yayan nasa ne bayan da ce-ce-kuce ta kaure a tsakaninsa da yayan nasa kan yanke wutar lantarkin da marigayin ya yi.
- Tinubu: Jonathan Ba Zai Kubutar Da Kai A Zaben 2023 Ba —PDP
- Gidauniyar Malam Inuwa Da Kokarinta Na Ilmantar Da Mutanen Karkara Da Rugage
Har ila yau, an ruwaito cewa, Peter yaki biyan bill din kudin na wutar da ya yi amfani da ita Naira 1,500 inda hakan ya sa aka datse wutar da Peter ke amfani da ita a dakinsa.
‘Yan uwan wadanda ke zama a gida daya, inda wata majiya ta ce, yanke wutar ta Peter ya tunzura shi shiga dakinsa ya dauko bindiga ya harbi yayan nasa mai suna Godwin, inda bayannan ya aikata kisan.