Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya karbi bakuncin tawagar Bankin Duniya da nufin karfafa hadin gwiwa kan mayar da ‘yan gudun hijira muhallinsu na asali.
Radda ya jaddada kudurin gwamnatinsa na sake gina rayuwar al’umma da kuma kula da wuraren da ke fama da matsalar tsaro. Ya bayyana goyon bayan Bankin Duniya a matsayin mafita ga ‘yan gudun hijira da al’ummomin da abun ya shafa da kuma tsare-tsaren hadin gwiwa wanda zai tabbatar da zaman lafiya mai dorewa ga mutane.
- Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja
- Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin
Gwamna Radda ya bayyana hakan yayin karbar bakuncin shugabannin tawagar Bankin Duniya, Mista Christoper Maya Johnson da wata kwararra jami’a, Hajiya Zara Goni Imam a Abuja.
Tawagar sun gabatar da kansu ga babban sakataren hukumar gudanarwar ci gaban Jihar Katsina, Dakta Mustapha Shehu. Tawagar sun ce ziyarar wani bangare ne na shirye-shiryen gudanar da aikace-aikace domin inganta zaman lafiya da kuma sanar da tallafin jin kai ga ‘yan gudun hijira.
Gwamnan Katsina ya yaba wa Bankin Duniya da ya yi hadin gwiwa da Jihar Katsina don fuskantar matsalolin tsaro da kuma tallafa wa ‘yan gudun hijira.