Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ya bukaci al’ummar Nijeriya su hada hannu da karfe da gwamnati wajen kawar da matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar nan, a yayin da kasar ke cika shekara 65 da samun ‘yancin kai.
A sakon taya murnar na ranar ‘yancin kai, Gwamna Radda ya taya al’ummar Jihar Katsina da dukkan ‘yan Nijeriya murnar cika shekara 65 da samun ‘yancin kai. Inda ya bayyana ranar a matsayin wata hanyar ci gaba, ya yi kira da a kara inganta aikace-aikacen da za su kara kawo ci gaba.
Ya yi nuni da cewa kasar nan na fuskantar kalubale, musamman yankunan da ke fama da matsalar tsaro, amman ya bayyana cewa matsalar tsaro za ta zama tarihi ta hanyar samun hadin kai.
Gwamna Radda ya jaddada cewa hukumomin tsaro kadai ba za su iya fada da ‘yan ta’adda ba, sai dai da gudummuwar ‘yan kasa. Ya yi kira ga ‘yan Nijeria da su zama masu sanya ido da kai rahotanni cikin gaggawa da bayar da ingantattun bayanai ga jami’an tsaro.
Ya yaba wa gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu bisa inganta tsaro da maido da martabar tattalin arzikin kasar nan.














