Wani matashi mai suna Mamuda Zakari Yau, mai shekaru 30 a duniya, ya shiga hannun ‘yansanda bisa zargin kashe wani ɗan Acaɓa, Basiru Mohammed, mai shekaru 25, tare da sace mashin ɗinsa domin samun kuɗin da zai ƙara auro mace ta uku.
Rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi, ta ce lamarin ya faru ne a unguwar Dakta Sulaiman Adamu, inda wanda ake zargi ya caka wa ɗan Acaɓan wuƙa sannan ya tsere da mashin ɗinsa ƙirar Bajaj Boxer mai lambar NNG 813 UM.
- Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA
- Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO
Kakakin ‘yansandan jihar, CSP Ahmed Wakil, ya ce marigayin ya rasu kafin a kai shi asibiti, yayin da aka kama wanda ake zargi bayan gano inda yake.
A yayin bincike, Mamuda ya amsa laifinsa, inda ya bayyana cewa son ƙaro mace ta uku ne ya tursasa shi aikata laifin.
Wakil, ya ce jami’an ‘yansanda sun gano wasu kayayyaki a waje. da abin ya faru, ciki har da wuƙar da aka yi amfani da ita, takalmi, da wayar salula.
Ya ce rundunar ta ɗauki matakai don tabbatar da adalci ga marigayin da iyalansa.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya umarci a miƙa lamarin sashen SCID domin zurfafa bincike da kuma gurfanar da wanda ake zargi a kotu.
A gefe guda kuma, ya gargaɗi matasa da su guji aikata laifuka saboda matsin tattalin arziƙi ko wasu dalilai na son zuciya.