Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, a ranar Litinin ya ce hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta kwato kadarorin da suka haura Naira biliyan 500 a cikin shekaru biyu na gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Shettima ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bude taron karawa juna sani karo na 7 na kwanaki uku ga alkalai wanda hukumar EFCC da cibiyar shari’a ta kasa suka shirya a Abuja.
A cewar mataimakin shugaban kasar, manufar gwamnatin na rashin tsoma baki a ayyukan hukumomin yaki da cin hanci da rashawa ya karfafa yaki da cin hanci da rashawa da kuma inganta ayyukan hukumomin.
“A matsayinmu na gwamnati, mun ba da fifiko ga al’amuran jama’a ta hanyar karfafa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da kuma ba su ‘yancin kai da ake bukata don aiwatar da ayyukansu na doka,” in ji Shettima wanda ya wakilci Shugaba Tinubu a wurin taron.