Limamin masallacin Juma’a na Bosso Estate kuma sakataren kungiyar limaman Juma’a a Jihar Neja, Dakta Umar Faruk Abdallah ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar an hukunta sojojin da suka kashe malamin addinin musulunci a Yobe Sheikh Goni Aisami don ya zama izina ga gurbatattun mutanen da ke fakewa da rigar kariya suna aikata ta’addanci da yunkurin kawo rashin zaman lafiya a kasa.
Dakta Abdullahi ya yi kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala sallar Juma’ar makon jiya.
- Ya Kashe Yayansa Kan Kudin Wutar Lantarki Naira 1,500 A Anambra
- Tinubu: Jonathan Ba Zai Kubutar Da Kai A Zaben 2023 Ba —PDP
Malamin ya ci gaba da cewa abin da wadannan bata-garin suka aiwatar cin amana da tarwatsa zaman lafiyar ne.
Ya ce “Ba maganar korarsu aiki muke saurare ba, a fito da su a hukunta su gaban jama’a domin ya zama darasi ga wadanda ke da mummunar akida irin tasu.”
“Muna kara yin kira ga al’umma da su fito su nuna rashin jin dadinsu, amma ba ma goyon bayan zanga-zanga ko daukar matakin da ya saba wa dokokin kasa”, in ji shi.
Da ya juya kan matsalar kuncin rayuwar da jama’a ke ciki kuwa, ya ce ya kamata gwamnati da sarakunan gargajiya da su dubi halin da jama’a ke ciki musamman wajen tsadar kayayyakin masarufi.
Shehin malamin ya ci gaba da cewa ya kamata gwamnati da sarakuna iyayen kasa da su sanya idanu a kan halin kuncin rayuwar da al’ummar kasar nan ke ciki, musamman bangaren kayayyakin masarufi domin saukakawa rayuwar talaka