Bisa tarin nasarorin da kasar Sin ta cimma karkashin shirye-shiryenta na raya kasa na shekaru biyar-biyar cikin shekaru sama da 70 da suka wuce, wato tun daga shirin karo na farko da aka kaddamar a shekarar 1953 zuwa yanzu, duk mai bibbiyar kasar zai gamsu da tasirin shirye-shiryen, duba da yadda suka bunkasa kasar a dukkanin fannonin ci gaban bil’adama. Kuma ko shakka babu shirin karo na 15 dake tafe ma zai bude wani sabon babi na kara bunkasa ci gaban kasar zuwa matsayi na gaba.
Idan muka kalli dukkanin lungu da sako na kasar Sin, muna iya ganin shaidu na zahiri dake nuna himma da kwazo da kasar Sin ta yi, har ta kai ga nasarori masu ban mamaki cikin wadannan shekaru, har zuwa yanzu da ake karkare shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14. Karkashin hakan, kasar Sin ta kai ga kyautata harkokin noma, da samar da isasshen abinci, ta tufatar da miliyoyin al’ummunta, ta kafa cikakken tsarin masanaantu da na tattalin arziki, kana ta samu ci gaba a fannonin raya ilimi, da kimiyya, da aladu, da kiwon lafiya da wasanni da sauransu.
Har ila yau, kasar ta kai ga bunkasa mizanin karuwar tattalin arziki na GDP na dukkanin al’ummunta. Kazalika, ta tunkari matsalolin hada-hadar kudade, inda ta kai zuwa kasa mai al’umma dake da matsakaiciyar wadata. A shirin karo na 14 dake daf da kammala kuwa, Sin ta yi rawar gani a fannin zamanintar da kai bisa tsarin gurguzu daga dukkan fannoni.
Yanzu haka kuwa, hankula na kara karkata ga shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 da Sin za ta aiwatar tsakanin shekarar 2026 dake tafe zuwa shekarar 2030, kuma masharhanta na ganin a karon gaba, Sin za ta fadada manufofinta na samar da ci gaba domin dorar da nasarorin da ta riga ta cimma.
Muhimman fannonin da ake ganin shirin na iya mayar da hankali a kansu, sun hada da tunkarar kalubalen karuwar kason al’ummar kasar masu tsayin shekaru, da kokarin warware tarnakin kasashen yamma dangane da harkokin cudanyar fasaha, yayin da Sin din ke fafada kirkire-kirkire a cikin gida.
Kamar yadda Sin ta riga ta dora dan-ba a fannonin zuba jari don cin gajiyar fannonin kimiyya da fasaha, da fasahohin kirkirarriyar basira ko AI, ta kuma kai ga samun manyan nasarori, a nan gaba ma ana fatan ganin karin ci gaban kasar a wadannan fannoni.
Har ila yau, wasu muhimman fannonin da aka ga kasar Sin na mayar da hankula a kai sun hada da samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da kyautata amfani da makamashi mai tsafta da inganci, da daidaita cin gajiya tsakanin ayyukan kare muhalli da na zamanintar da tattalin arziki.
Fatan dukkanin sassan Sin, da ma masu burin nasarar kasar shi ne kamar yadda shirye-shiryenta na raya kasa na shekaru biyar-biyar guda 14 suka yi nasara, shi ma shirin karo na 15 zai cimma nasarar da ake fata, ga ita kanta Sin da ma sauran sassan duniya abokan tafiyarta.(Saminu Alhassan)














