Shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), ya jagoranci wani taron karawa juna sani a ranar 27 ga watan Augusta, domin jin ra’ayoyin wadanda ba ‘yan jam’iyyar ba, dangane da shawarwarin da kwamitin kolin JKS ya gabatar game da tsara shirin raya kasa na shekaru 5 karo na 15, da ke da nufin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar. (Fa’iza Muhammad Mustapha)












