Za a gudanar da kwarya-kwaryan taron shugabannin kungiyar APEC karo na 32 a Koriya ta Kudu.
Eduardo Pedrosa, babban daraktan sakatariyar APEC, ya bayyana cewa tun bayan shigarta APEC, Sin ta kasance mamba mai himma da kwazo. Kuma a halin yanzu, tana taka muhimmiyar rawa wajen ba da jagoranci a karkashin tsarin APEC, haka kuma tana mai da hankali kan yadda za a inganta samar da manyan ci gaba a yankin da kuma duniya baki daya.
Eduardo Pedrosa ya bayyana haka ne kwanan nan yayin wata hira da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG a birnin Gyeongju dake Koriya ta Kudu. Ya kuma yaba da nasarorin da Sin ta samu a tafarkinta na zamanantar da kanta.(Safiyah Ma)
 
			




 
							








