Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta sanar da jerin sakamakon da aka cimma, yayin tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin tawagar kasar da ta Amurka, wadda ta gudana a baya bayan nan a birnin Kuala Lumpur.
Bayanan ma’aikatar cinikayyar sun nuna cewa, Amurka ta amince da soke kaso 10 bisa dari na harajin da ta ce za ta kakabawa Sin dangane da batun sinadarin fentanyl, kana za ta dage kaso 24 bisa dari na harajin ramuwa da ta yi aniyar dorawa kan hajojin Sin dake shiga Amurka da karin shekara guda, ciki har da hajojin yankin musamman na Hong Kong, da Macao. A cewar kakakin ma’aikatar cinikayyar Sin, a nata bangare Sin za ta daidaita nata matakan na mayar da martani da ta ayyana, bayan da Amurka ta ambata nata matakan, kuma sassan biyu sun amince su ci gaba da tsawaita matakan kawar da haraji kan wasu hajoji da suka amincewa.
Kazalika, Amurka ta amince za ta jingine aiwatar da wata sabuwar ka’ida da ta ayyana a ranar 29 ga watan Satumban bana da karin shekara daya, ka’idar da ta fadada jerin abubuwa da aka kakabawa takunkumai na fitarwa zuwa duk wani bangare dake karkashin mallakin kaso a kalla 50 bisa dari, na bangare daya, ko sama da daya cikin jerin bangarorin da aka sanya cikin jadawalin baya. Bugu da kari, Sin za ta dage wajen aiwatar da matakai masu nasaba da ta sanar a ranar 9 ga watan nan na Oktoba da karin shekara daya, kuma za ta nazarci tsare-tsaren aiwatarwa na musamman na kasar.
A nata bangare, Amurka za ta dage aiwatar da matakai bisa bincikenta karkashin sashe na 301 na dokar cinikayya ta 1974, wanda zai shafi sashen jiragen ruwa na Sin, da hidimomin sufurinsu, da na kirar jiragen ruwan na Sin da karin shekara daya. Sakamakon hakan, ita kuma Sin za ta dage aiwatar da matakan martani ga sashen Amurka a wannan fanni da shekara daya, da zarar Amurkan ta aiwatar da na ta matakan.
Kakakin ya ce “An Kai Ruwa Rana” kafin cimma wannan sakamako, kuma Sin na fatan ganin ta ci gaba da aiki tare da tsagin Amurka, ta yadda za su hada karfi wajen tabbatar da an aiwatar da sakamakon, da ingiza karin tabbaci, da daidaito cikin dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu, da kuma tattalin arzikin duniya baki daya. (Saminu Alhassan)
 
			




 
							







