A ranar Litinin jami’an tsaro da dama sun hallara a hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja yayin da Abdulrahman Mohammed Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa (Arewa ta Tsakiya), ya yi ikirarin cewa, ya karɓi mukamin Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar na Kasa a yayin da rikicin shugabancin Jam’iyyar ke kara tsananta.
Kwamitin gudanarwar jam’iyyar na ƙasa (NWC) da ke ƙarƙashin jagorancin Samuel Anyanwu ne ya naɗa Mohammed a matsayin muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar na ƙasa bayan sauke Umar Damagum, da Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba, a matsayin wani mataki na adawa da NWC da Damagum ke jagoranta suka yi a baya.
Kafin isa sakatariyar PDP da ke Wadata Plaza, Mohammed da magoya bayansa sun taru a ofishin jam’iyyar na Babban Birnin Tarayya (FCT), inda ya tabbatar da sabon matsayinsa kuma ya yi wa ‘ya’yan jam’iyyar jawabi.
“A yau, mun dauki nauyin dawo da tsari da hadin kai a cikin babbar jam’iyyarmu,” in ji shi. “PDP ta ‘ya’yanta ce, kuma babu wani mutum ɗaya tilo da zai riƙa juya ta yadda yake so.”














