Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta ce wasu shugabannin kasashen waje za su hallara a birnin Shanghai, domin halartar baje kolin hajojin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE karo na takwas, wanda zai gudana tsakanin ranakun 5 zuwa 10 ga watan nan na Nuwamba.
Kakakin wadda ta bayyana hakan a Litinin din nan, ta ce cikin shugabannin da ake sa ran za su halarci bikin bude baje kolin na CIIE, da sauran ayyuka masu nasaba da shi bisa gayyatar da aka yi musu, akwai firaministan kasar Georgia Irakli Kobakhidze, da na Serbia Djuro Macut, da kakakin majalisar wakilan tarayyar Najeriya Abbas Tajudeen, da shugaban majalisar gudanarwar kasar Slovenia Marko Lotric. (Saminu Alhassan)
			




							








