Yau 3 ga wata, aka bude taron kasuwanci na duniya na 18 a Macau dake kudancin kasar Sin. Wang Huning, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, ya aika sakon gaisuwa, inda ya yi murna da gudanar da taron kuma ya gaida wakilan ‘yan kasuwa na Sin a duniya, da Sinawan dake gida da ketare da sauran mutane mahalarta.
Wang ya bayyana cewa, a tsawon lokaci, ’yan kasuwa Sinawa a duniya sun shiga an dama da su cikin ayyukan gyare-gyare a cikin kasar Sin da kokarin zamanintar da al’ummar Sinawa, kuma suna habaka kyawawan al’adun gargajiya na Sin, tare da ba da gudummawa mai muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar Sin, da huldar kasuwanci da al’adu tsakanin Sin da sauran kasashe.
Ya kuma yi fatan cewa baki za su yi amfani da wannan taro a matsayin dama don neman sabbin hanyoyin hadin gwiwa da kirkirar sabbin wuraren ci gaba, don kara wa duniya kwarin gwiwa. Haka kuma, ya yi fatan ’yan kasuwa na Sin za su yi amfani da fa’idodinsu da damarmaki don taka rawar gani wajen habaka hadin gwiwar kasuwanci da fasaha da musayar al’adu tsakanin Sin da sauran kasashe, da kuma ba da gudunmawarsu wajen taimakawa farfado da al’ummar Sinawa da samun sabbin ci gaba. (Amina Xu)
			




							








