Yau 5 ga Nuwamba, kwamitin haraji na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya ba da wata sanarwar cewa, daga ranar 10 ga Nuwamba, 2025, da karfe 13:01, Sin za ta yi gyara kan matakan haraji da kwamitin ya gabatar a baya kan kayayyakin da za a shigo da su daga Amurka, wato sanarwar kwamiti mai lamba 4 ta shekarar 2025, bisa ga dokar haraji ta jamhuriyar jama’ar Sin, da dokar kwastam ta Sin, da kuma dokar cinikin shige da fice da dai sauran dokoki da ka’idojin kasa da kasa, tare da amincewar majalisar gudanarwar kasar, don aiwatar da yarjejeniyar ciniki tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata.
Sanarwar ta ce, a cikin wannan shekara guda mai zuwa, za a ci gaba da dakatar da karin haraji na kashi 24% a kan kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka, yayin da za a ci gaba da sanya haraji na kashi 10%.
A wata sabuwa kuma, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta sanar a yau Laraba cewa, a yayin aiwatar da yarjeniyoyin da aka cimma ta hanyar tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysiya, kasar Sin za ta ci gaba da dakatar da matakin da ta dauka a kan jerin sunayen kamfanoni marasa aminci na tsawon shekara guda, daga ranar 10 ga watan Nuwamba, wanda mataki ne da ta sanar da daukawa a ranar 4 ga Afrilun wannan shekara, da ya shafi wasu kamfanonin Amurka.
Haka kuma, daga ranar 10 ga watan Nuwamba, kasar Sin za ta soke matakin da ta dauka a kan wasu kamfanonin Amurka a cikin jerin kamfanoni marasa aminci da ta sanar a ranar 4 ga Maris na wannan shekara, kamar yadda wani mai magana da yawun ma’aikatar ya bayyana a cikin wata sanarwa.
Mai magana da yawun ma’aikatar ya kara da cewa kamfanonin cikin gida za su iya gabatar da bukata da neman yin ciniki da kamfanonin Amurka da aka ambata a sama da zarar an amince da bukatunsu. (Amina/Abdulrazaq Yahuza Jere)














