A yau Laraba 5 ga wata ne firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci taron bude bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin CIIE karo na 8 da kuma dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya na Hongqiao a Shanghai da ke gabashin kasar Sin, inda ya gabatar da jawabi.
A cikin jawabinsa, Li Qiang ya ce, kamar yadda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya fada, tattalin arzikin kasar Sin kamar babban teku yake, haka ma na duniya, yana mai cewa, tattalin arzikin Sin da na duniya suna hade da juna. Ya ce, bikin CIIE ya hada kasar Sin da kasashen duniya. Yawan kamfanonin da suka halarci bikin na bana ya kai matsayin koli a tarihi, lamarin da ya nuna babbar kasuwar kasar Sin mai karfi da kuzari.
Li ya ci gaba da cewa, wani muhimmin dalilin da ya sa aka gudanar da bikin na CIIE har sau 8 shi ne domin gabatar da damar samun riba ga kasa da kasa. Ya kuma bayyana ra’ayinsa daga fannoni guda 3 dangane da lamarin, wato, da farko tabbatar da adalci da samun moriyar juna, da inganta halastacciyar moriyar bai daya. Na biyu, kiyaye gaskiya da adalci tsakanin kasa da kasa, na uku, kara azama kan yin gyare-gyare a harkokin shugabanci, a kokarin kyautata tsarin ka’idojin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa.
Firaministan kasar Georgia Irakli Kobakhidze da firaministan kasar Serbia Duro Macu da shugaban majalisar wakilan kasar Najeriya Tajudeen Abbas, sun halarci taron bude bikin tare da ba da jawabai. Haka kuma wakilai kimanin 1500 daga sassan siyasa, kasuwanci da ilmi na kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa 155 su ma sun halarci taron.(Tasallah Yuan)














