An rufe bikin baje kolin harkokin cinikayya na birnin Guangzhou da aka fi sani da Canton Fair, karo na 138 jiya Talata a Guangzhou. Wannan biki ya sami halartar masu sayayya sama da 310,000 daga kasashe da yankuna 223, wanda ya karu da kashi 7.5 cikin 100 idan aka kwatanta da na baya, inda ya kafa sabon tarihi. Yawan kudin da aka yi hasashen kashewa wajen fitar da kayayyaki a yayin bikin ya kai dala biliyan 25.65.
Bisa kididdigar masu shirya bikin, masu sayayya na kasashen da ke cikin shawarar “ziri daya da hanya daya” sun kai 214,000, wanda ya karu da kashi 9.4 cikin 100. Kasuwar fitar da kayayyaki tsakanin mahalarta bikin da kasashen da ke cikin shawarar ta kai sama da kashi 60 cikin 100, yayin da kasuwar kasashen da suka saba halartar bikin, ta ci gaba da habaka cikin kwanciyar hankali.
Bikin ya gabatar da sabbin kayayyaki guda 632. Sabbin kayayyakin da aka samar ba tare da bata muhalli ba da kayayyakin fasaha sun kai sama da kashi 20 cikin 100 daga cikin kayayyaki miliyan 4.6 da aka nuna. Mutum-mutumin inji masu siffar bil adam, na’urori masu kwakwalwa, kayayyakin da aka samar daga halittu, na’urorin jinya na AI, da na bugu irin na 3D da sauransu, sun zama kayayyakin da suka fi samun karbuwa a wajen bikin. (Amina Xu)














