Karin karfi da kasashe masu tasowa suka samu a tare, ya ba su karin dama ta shiga a dama da su cikin tafiyar da harkokin duniya, lamarin da ya bude wata kafa ta haskawar kasashe masu tasowa a ayyukan tafiyar da harkokin duniya.
Wani nazari da kafar CGTN ta kasar Sin ta kaddamar, wanda ya shafi mutane 9,182 a kasashe 47 na fadin duniya, ya nuna cewa masu bayar da amsa daga kasashe masu tasowa sun yi kira da a inganta tare da aiwatar da sauye-sauye a tsarin tafiyar da harkokin duniya na yanzu, kuma sun yaba wa shawarar Tafiyar da Harkokin Duniya da kasar Sin ta gabatar, suna masu sa ran za ta kara taka rawa a tsarin na tafiyar da harkokin duniya.
Game da muhimman kalubalen da ake fuskanta cikin tsarin tafiyar da harkokin duniya a yanzu, masu bayar da amsa na kasashe masu tasowa sun bayyana fatara da rashin tsaro da wadatar abinci a matsayin manyan batutuwa 3 dake ci wa duniya tuwo a kwarya, inda kashi 74 suka zabi fatara da rashin daidaito, kashi 70.9 kuma sun zabi rashin wadatar abinci, sai kashi 63.6 da suka zabi ayyukan ta’addanci da rashin tsaro a yankuna.
Haka kuma, kaso 73.2 sun yi imanin cewa manyan kasashe ba sa sauke dukkan nauyin da ya rataya a wuyansu game da harkokin kasa da kasa, sannan kaso 81.9 sun yi kira ga MDD da ta kara mayar da hankali kan muradu da bukatun kasashe masu tasowa. (FMM)














