Na san da yawa idan aka ce “yanayi mai launin zinare” wasu za su dauka, ado ne ake yi da kayan alatu na zinare daban-daban domin kawata wasu kebantattun wurare don su zamo masu kyawun gani, musamman bisa yadda kasar Sin ke ci gaba da kawata biranenta don su amsa sunansu a duniya. Sai dai, a wannan gabar, ba haka abun yake ba.
“Yanayi mai launin zinare” da ake nufi shi ne lokacin kaka, yayin da bishiyoyi musamman a yankunan arewacin kasar Sin suka juya ganyayyakinsu zuwa launin zinare domin shirin sabon tofo ko yanayin da wasu ke wa lakabi da “lokacin kakkaba”.
A kwanan nan, ni da wani abokin aikina mun fita don yin tattaki a birnin Beijing na kasar Sin a karshen makon da ya gabata, ga mamakina: sai na ga yanayin birnin ya sauya sakamakon launin zinare da ya bayyana a ganyayyakin bishiyoyin da aka daddasa a sassan birnin. Kuma abun da ya kara wa yanayin kyau shi ne, akwai wasu bishiyoyi da ganyayyakinsu ke bayar da wasu launuka daban da aka ratsa a tsakanin masu launin zinaren.
A gaskiya wannan yanayi ya yi matukar burge ni, kuma sai na zaci ko don saboda ina bako ne, amma yayin da na ga wasu Sinawa suna daukar hotunan bishiyoyin, sai na ce to, babu makawa wannan yanayi ne mai burge kowa da kowa, bako da dan gari kuma ciki har da dattawa. Nan take ni ma na zaro wayata, muka ci gaba da kashe hotuna ni da abokin aikina. Na yi kokarin nuna kawaici a kan yadda yanayin ya shaukantar da ni, amma sai na ga abokin nawa ya fi ni “jazabancewa”, domin shi ya fi ni yawan yin “style” na daukar hoton da kuma yawan hotunan da muka dauka.
Wani abu da na lura da shi a kasar Sin shi ne, ba kawai a manyan birane ba, hatta a garuruwa na gundumomi, kasar ta samar da lambuna masu furanni da koramu da itatuwa masu ban sha’awa, inda iyalai suke zuwa domin shakatawa musamman da maraice bayan tasowa daga makaranta.
Ni dai, idan wani mai yawon shaktawa ya tambaye ni, wane lokaci ne mafi dacewa ya kawo ziyara kasar Sin, zan ce masa ka zo a lokacin “yanayi mai launin zinare”, watau a lokacin kaka, musamman daga karshen watan Oktoba kafin shiga yanayin hunturu sosai lokacin da wannan launi zai sauya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














