A yau Laraba 5 ga watan Nuwamba, an bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin na kasa da kasa (CIIE) karo na 8 a birnin Shanghai. A yayin wani taron manema labarai na yau da kullum da ya gudana a wannan rana, mai magana yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta nuna cewa, nasarar karbar bakuncin bikin baje kolin CIIE tsawon shekaru takwas a jere ta nuna kudurin kasar Sin da ayyukanta na cika alkawarinta na bude kofa, da kuma cimma burin samun moriyar juna da kuma nasara ga kowane bangare.
Mao Ning ta bayyana cewa bikin baje kolin na CIIE shi ne babban baje kolin kayayyaki a matakin na kasa na farko a duniya wanda ke da jigon shigo da kayayyaki daga waje, kuma wani sabon salo ne da yunkuri mai alfanu ga kasar Sin don ta fadada bude kofa ga sauran kasashe.
Girman bajen kolin CIIE na wannan shekarar ya gawurta zuwa sabon matsayi, inda kamfanoni sama da 4100 daga kasashen waje suke halarta. Harka tare da kasar Sin tamkar mabudi ne na samun damammaki, wanda hakan ya samu ittifakin amincewa a tsakanin dukkan bangarorin da suke halarta. Kasar Sin za ta ci gaba da fadada bude kofa da kuma sanya babbar kasuwarta ta zamo babbar dama ga duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)













