Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a yi cikakkiyar zurfafa gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje domin samun ci gaba mai inganci, da kuma bunkasa ci gaban yankin Guangdong-Hong Kong-Macao ta hanyar dorewar kokarin da ake yi.
Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kwamitin koli na soja, ya yi wannan jawabi ne a lokacin rangadin aikin da ya yi a lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin a jiya Jumma’a da kuma yau Asabar.
A lokacin da ya ziyarci lambun tunawa da Ye Jianying da ke birnin Meizhou a ranar Jumma’a da rana, Xi ya yi nuni da cewa dukkan manyan nasarorin da kasar Sin ta samu a yau an gina su ne bisa harsashin da Mao Zedong da sauran tsoffin ‘yan juyin juya hali suka kafa, yana mai kira da a yi kokari wajen ilmantar da jami’ai da sauran al’umma, musamman matasa don ci gaba da aiwatar da dabi’un juyin juya hali.
Duk dai a Meizhou, Xi ya kuma ziyarci wata cibiyar noman lemun pomelo inda aka yi masa bayani game da kokarin da Guangdong ke yi na kara tallafa wa tsoffin wuraren juyin juya hali da kuma ci gaba da farfado da yankunan karkara a ko ina, da sauransu.
A safiyar yau Asabar kuma, shugaba Xi ya duba baje kolin nasarorin da lardin ya samu a fannin ci gaban fasaha da kirkire-kirkire a babban birnin lardin Guangzhou. Bayan haka, Xi ya saurari rahoton aiki daga kwamitin jam’iyya da gwamnatin lardin Guangdong.
Xi ya jaddada cewa, domin lardin Guangdong ya samar da sabbin damammaki da cimma sabbin nasarori, ya zama dole a ci gaba da himma wajen aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa, da aiki da ruhin yankunan tattalin arziki na musamman, da kuma karfafa samun ci gaba mai inganci ta hanyar zurfafa gyare-gyare da bude kofa.
Ya yi kira da a yi kokarin zurfafa hadin gwiwa tsakanin Guangdong, Hong Kong da Macao, da kuma tallafa wa inganta hadewar Hong Kong da Macao da kuma hidimta wa ci gaban kasar baki daya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














