A bana ne ake cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya na kin tafarkin murdiya, gami da kawo karshen mulkin mallakar kasar Japan a yankin Taiwan da dawo da shi kasar Sin. Kwanan nan ne CMG wato babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin ya wallafa jerin wasu rahotannin talabijin guda biyar dangane da batun dawowar Taiwan kasar Sin.
’Yan jarida ma’aikatan CMG ne suka dauki rahotanni da bidiyo a yankin Taiwan, inda suka yi amfani da kwararan shaidun tarihi, don mayar da martani ga wasu kalaman karya da ke cewa wai “matsayin Taiwan ba shi da tabbas”, tare kuma da bankado markarkashiyar mahukuntan jam’iyyar DPP na yankin Taiwan ta yabawa da mulkin mallaka da Japan ta yi da boye gaskiyar tarihi.
Rahotannin na talabijin sun samu babban yabo daga bangarori daban-daban na yankin Taiwan, inda jama’ar yankin ke kira ga mahukuntan Taiwan, da su mutunta gaskiyar tarihi, da daina yaudarar jama’ar Taiwan. (Murtala Zhang)














