Mataimakin firaministan kasar Sin Ding Xuexiang ya fada a ranar Alhamis da ta gabata cewa, a duk irin yadda yanayin kasa da kasa ya sauya, kasar Sin za ta tsaya kyam a kan sahihiyar manufar hadin gwiwa tsakanin mabambantan bangarori, kana za ta ci gaba da goyon bayan muhimmiyar rawar da Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ke takawa a harkokin kasa da kasa.
Ding, a matsayin wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi wannan tsokaci ne a lokacin ganawarsa da babban sakataren MDD Antonio Guterres a gefen taron sauyin yanayi na Belem.
A nasa bangaren, Guterres ya nuna godiyarsa ga kasar Sin bisa goyon bayan da take bai wa ayyukan MDD a-kai-a-kai, sannan ya yaba da nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin bunkasa ci gaba mara gurbata muhalli, yana mai cewa kasar Sin ta cika alkawuran da ta dauka, kuma ta dauki matakai har ma fiye da na alkawuran da ta dauka wajen magance sauyin yanayi. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














