An bayyana farfesa Chukwuma Soludo na jam’iyyar APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Anambra da aka kammala a ranar Asabar.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta sanar da cewa an tattara kuri’u daga dukkan kananan hukumomi 21 na jihar, inda jimillar kuri’un da aka tantance suka kai 584,054. Daga cikin Soludo ya samu kuri’u mafi rinjaye 422,664.
- Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga
- Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura
Ɗan takarar jam’iyyar APC, Nicholas Ukachukwu, ya zo na biyu da kuri’u 99,445, yayin da jam’iyyar ADC ta samu 8,208, sannan PDP ta samu 1,401.
Babban mai tattara zaɓe da hukumar ta turo, Farfesa Edogah Omoregie, kuma shugaban jami’ar Benin, shi ne ya karanta sakamakon na karshe a hedkwatar zaɓe da ke Awka.
Nasarar Soludo ta nuna cewa APGA na ci gaba da daƙile siyasar yankin, tare da samun cikakken goyon bayan jama’ar jihar.














