Wani masani dan kasar Zimbabwe Tungamirai Eric Mupona ya bayyana cewa, hadin gwiwar da kasar Sin ke yi da kasashen Afirka ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaba da habaka bunkasar nahiyar.
Mupona, wanda yake mataimakin shugaban Cibiyar musaya da cudanya tsakanin kasashen Sin da Zimbabwe, wata kungiya mai zaman kanta da ta sadaukar da kai ga ci gaban al’adu da tattalin arziki a tsakanin Sin da Zimbabwe, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a wata hira da ya yi kwanan nan cewa, kasar Sin ta tashi daga kasancewa babbar abokiyar ciniki ta Afirka zuwa matakin kulla cikakken hadin gwiwa mai karfi da kasashen Afirka, wanda ya kawo moriya masu yawa ga nahiyar.
Ya kara da cewa, “Kasar Sin tana kawo jari, da kwarewa, da fasaha da aka fi bukata sosai a nahiyar, tana kuma habaka masana’antun nahiyar ta hanyar saka hannun jari a kamfanoni, da bunkasa ababen more rayuwa, da sarrafa ma’adanai, da sauran fannoni masu mahimmanci.”
Ya yaba da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya (BRI) da Sin ta tsara, yana mai cewa shawarar ta kasance mabudin zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Afirka, da karfafa hadin gwiwa a sauran fannoni, da kuma samar da moriya mai amfanarwa a sassan nahiyar.
Kazalika, Mopuna ya ce, “Baya ga wadannan jarin daban-daban da ke shigowa, Sin ta ci gaba da bude kasuwarta ga kayayyakin Afirka a cikin ‘yan shekarun nan,” inda ya kara da cewa, wadannan matakan sun samar da “karin tagomashi” ga kayayyakin noma na Afirka kuma sun ba manoman yankin damar samun karin kudin shiga. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














