Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina ta musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa magoya bayan Katsina United sun kashe ɗan wasan Barau FC, Nana Abraham, yayin wasan gasar NPFL a mako na 12 a filin wasa na Muhammadu Dikko, Katsina.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar, ya ce labarin ƙarya ne kuma makirci ne domin tayar da hankalin jama’a.
- HOTUNA: Yadda Gobara Ta Ƙone Shaguna 25 A Kasuwar Singa A Kano
- Faɗa Ya Kaure Tsakanin Boko Haram Da ISWAP, An Kashe Mayaƙa Sama Da 170
‘Yansanda sun tabbatar da cewa Nana Abraham yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana samun kulawar likitoci.
Bincike ya nuna cewa babu wata arangama da ta faru tsakanin magoya baya ko ‘yan wasa a lokacin ko bayan wasan.
Rundunar ta ce shugabannin NPFL sun yi duba a kan wasan tare da ɗaukar mataki a kan Katsina United bisa wasu laifuka, amma babu rahoton tashin hankali ko kisa da ya faru.
DSP Aliyu ya gargaɗi jama’a da su guji yaɗa labaran ƙarya, inda ya bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin aikata hakan za a hukunta shi.
Ya kuma roƙi mutane su dogara da sahihan bayanai daga hukumomi, tare da tabbatar da cewa rundunar ‘yansandan ƙarƙashin CP Bello Shehu tana ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar.














