An kaddamar da babbar hanyar mota mai suna “Dr. Hage G. Geingob Freeway”, wadda kasar Sin ta samar da kudaden tallafin kammalawa a birnin Windhoek fadar mulkin kasar Namibia.
A jiya Litinin ne aka kaddamar da katafaren aikin mai kunshe da sassa uku, aikin da ya kasance mai matukar muhimmanci a fannin inganta harkar sufuri a yankin tare da bunkasa tattalin arzikin kasar ta Namibia.
Gwamnatin Namibia ce ta samar da kudaden ginin kashi na daya da na biyu na tagwayen hanyoyin a shekarun 2016 da 2020, kana kamfanin gine-gine na Zhong Mei Engineering Group na kasar Sin, ya gina sashe na uku na hanyar a shekarar 2021, da tallafin kudade har yuan miliyan 447, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 62.8 daga gwamnatin kasar Sin.
An mika kashi na uku na aikin hanyar mai tsawon kilomita 21.3 da aka yiwa lakabi da Phase 2B a jiya, bayan kammala sanya hannu kan takardun shaidar kammalarsa.
Yayin da aka bude babbar hanyar motar mai tagwayan layuka, lokacin sufuri daga wajen birnin Windhoek zuwa filin jirgin sama na kasa da kasa na Hosea Kutako ya ragu, daga mintuna kusan 50 zuwa kusan mintuna 20 kacal, lamarin da zai yi matukar inganta, da saukaka cunkoson ababen hawa a babban birnin kasar. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














