Jakadu da sauran jami’an diplomasiyya dake kasar Sin, sun bayyana shawarwarin da manyan shugabannin kasar Sin suka bayar wajen tsara shirin raya kasa na shekaru 5-5 na 15, a matsayin wadanda suke dauke kyakkyawan sako dake nuna wa duniya cewa, Sin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen fadada bude kofarta da samar da damarmaki ga duniya.
Jakadun sun bayyana haka ne bayan halartar wani taron karin haske game da zama na 4 na kwamitin kolin JKS na 20, wanda ya gudana a watan da ya gabata, tare da amincewa da shawarwarin kwamitin na tsara shirin raya tattalin arziki da zamantakewa a kasar Sin daga shekarar 2026 zuwa 2030.
Jakadun sun ce suna da cikakken kwarin gwiwa game da makomar ci gaban kasar Sin, inda suka bayyana cewa, a shirye kasashensu suke su zurfafa musaya da hadin gwiwa da Sin da hada hannu wajen inganta zaman lafiya da ci gaba a duniya.
Manyan jami’an diplomasiyya daga kasashe sama da 160, ciki har da jakadu 90 dake kasar Sin da manyan jami’an ofisoshin jakadancin kasashen ne suka halarci taron, wanda sashen kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS ya shirya. (Mai fassara: FMM)














