An kammala bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin (CIIE) na 8 a jiya Litinin, inda aka kulla cinikin dalar Amurka biliyan 83.49 a cikin yarjejeniyoyin da aka cimma, adadin da ya karu da kashi 4.4 cikin dari idan aka kwatanta da na baya kuma ya kai wani sabon matsayi.
Shin me hakan yake nufi?
Yayin baje kolin, an gabatar da sabbin kayayyaki da fasahohi da ayyuka har 461, kuma wannan shi ne karo na farko da aka gabatar da wasu daga cikinsu a duniya. Wannan alama ce cewa, masu kamfanoni da kere-kere suna daukar kasar Sin a matsayin kofar ta shiga kasuwannin duniya, domin ta zama wata hanya ta saukaka musu tallata kayayyakinsu. CIIE ya zama wani dandali na gabatar da kayayyaki ga sassan duniya, ba kasar Sin kadai ba.
Wannan shi ne baje koli na farko bayan taron kwamitin kolin JKS da ya amince da shirin raya kasa na shekaru 5-5 karo na 15, wanda ya jaddada kudurin Sin na fadada bude kofarta. Halartar kamfanoni da adadinsu ya kai 4,108, daga manya da matsakaita da kananan kasashe ya tabbatar da cewa, kofar Sin a bude take ga kasa da kasa su shigo, su yi cudanya da hadin gwiwa domin samun ci gaba na bai daya. Karuwar adadin mahalarta tamkar kira ne cewa, duniya ta amince kuma tana goyon bayan manufofi da tsare-tsaren kasar Sin. Haka kuma, goyon baya ne ga kiran kasar Sin na dunkule tattalin arzikin duniya da bunkasa cudanyar bangarori daban-daban domin samun ci gaba tare. Bugu da kari ya nuna cewa, bude kofa hanya ce ta samun habakar tattalin arziki da karin gogewa, da takara mai tsafta cikin ’yanci da samun damarmaki, maimakon kariyar ciniki da yakin haraji da dakile ci gaban wasu domin samun riba. (Fa’iza Mustapha)














