Majalisar Wakilai ta yanke shawarar kafa wani kwamiti na wucin gadi don binciko kadarori mallakar gwamnatin tarayya da suka hada da filaye da gine-gine da aka yi watsi da su a faɗin ƙasar, waɗanda aka ruwaito darajarsu ta kai sama da Naira tiriliyan 20.
Wannan ya biyo bayan amincewa da wani kudiri na gaggawa wanda Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda (PDP, Ribas), ya ɗauki nauyinsa a zaman majalisar na ranar Laraba.
- Lambar Yabo Da LEADERSHIP Ta Ba Mu, Ta Ƙara Zaburar Da Mu – Gwamna Sule
- Gwamnati Ta Janye Buƙatar Amfani Da Harshen Gida Wurin Koyarwa A Makarantu
Chinda, ya yi amfani da Umarni na 8, Doka ta 5 ta Dokokin Majalisa da Sashe na 88 da 89 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), ya ce, dole a yi binciken don hana ƙarin ɓarnatar da albarkatun jama’a da kuma tabbatar da dawo da kadarorin ƙasa masu mahimmanci.
Ya yi nuni da rahoton 2021 da Cibiyar Binciken kasa ta Nijeriya ta fitar, wanda ya gano kimanin filaye da gine-ginen gwamnatin tarayya 11,866 da aka yi watsi da su a duk faɗin ƙasar.
Daga cikin manyan kadarorin da ɗan majalisar ya lissafa akwai Cibiyar Sakatariyar Tarayya da ke Ikoyi, Legas; Ginin Otal na Ƙasa da Ƙasa na Nijeriya, Suleja, Jihar Neja; Millennium Tower, Abuja; Ginin Hukumar Haraji ta Tarayya a Jihar Abia; Hedikwatar Dakin karatu na Ƙasa, Abuja; Kamfanin Masana’antar buga Labarai na Nijeriya, Kaduna; Ginin Masaƙa ta Kaduna; da Kamfanin Narka Alluminium na Nijeriya, Jihar Delta.














