Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) reshen Jihar Kaduna ta ƙona miyagun ƙwayoyi masu nauyin kilo 52,481 da ta kama daga wurare daban-daban na jihar.
An gudanar da bikin ƙona waɗannan ƙwayoyi ne a garin Kufena, kusa da hanyar Birnin Gwari a Zariya, ranar Alhamis.
- An Kafa Cibiyar Kiwon Lafiya Ta Hadin Gwiwa Ta Farko Tsakanin Sin Da Afirka A Guinea
- Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim – Tanimu Akawu
Wannan mataki na daga cikin hanyoyin da hukumar ke amfani da su domin rage yaɗuwar miyagun ƙwayoyi da kuma kare al’umma daga illolinsu.
Ƙwayoyin da aka ƙona sun haɗa da wiwi, hodar iblis, methamphetamine, da wasu ƙwayoyi masu illa ga ƙwaƙwalwa.
An gudanar da taron ne a gaban jami’an tsaro, wakilan gwamnati, da shugabannin al’umma domin nuna haɗin kai wajen yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi.
NDLEA ta bayyana cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen yaƙar wannan matsala, tare da wayar da kan jama’a da kula da masu fama da shan ƙwayoyi, domin kare tsaron rayuka da zaman lafiya a ƙasar nan.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai wakilin shugaban NDLEA, Birgediya Janar Muhammadu Buba Marwa (mai ritaya), wato Kwamanda Muhammadu Tukur; wakilin Gwamnan Jihar Kaduna, da wakilin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, wato Alhaji Umar Muhammad Fagacin Zazzau.
Haka kuma, Kwamandan NDLEA na Jihar Kaduna da wakilai daga ‘yansanda, sojoji, DSS, da sauran hukumomin tsaro sun halarta.
Masu jawabi a wajen taron sun nuna farin ciki da wannan nasara, tare da yabawa jami’an tsaro, alƙalai, da jama’ar gari bisa gudunmawar da suka bayar.
An kammala taron lafiya, kuma kowa ya watse lafiya.














