Yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Comoros Azali Assoumani, sun aika wa juna sakon taya murnar cika shekaru 50 da kulla alakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.
A cikin sakonsa, shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, yana mayar da hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Comoros, kuma yana son hada hannu da shugaba Azali, da amfani da cikar alakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu shekaru 50, a matsayin wata dama ta ciyar da dangantakarsu ta gargajiya gaba, da ma inganta tabbatar da nasarorin da aka cimma a yayin taron koli na Beijing na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC), da bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Comoros bisa manyan tsare-tsare, da kuma kara taka rawar gani wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta Sin da Afirka ta ko wane lokaci a sabon zamani.
A nasa bangaren, shugaba Azali ya bayyana cewa, bisa yanayin da duniya ke ciki na fuskantar sauye-sauye da rikice-rikice, ra’ayin da shugaba Xi Jinping ya gabatar na girmama ikon mulkin kai da rashin tsoma baki cikin harkokin gidan kasa da kasa tare kuma da cimma nasara tare ta hanyar hadin kai, ya kara wa kasashe masu tasowa kwarin gwiwa, ciki har da kasar Comoros. Ya ce kasarsa na son yin kokari tare da kasar Sin bisa ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam, don karfafa samun dauwamamman ci gaba irin na hakuri da juna, da ba da gudummawa ga inganta hadin kai da ma samun wadata tare a tsakanin Afirka da Sin. (Bilkisu Xin)














