An gudanar da taro mai taken “Shugabancin Duniya: Ayyukan Matasa”, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya dauki nauyi, a Johannesburg dake Afirka ta Kudu a ranar 11 ga wata. Jigon taron shi ne, “Matasa su tattauna kan tsarin shugabancin duniya, kuma su hada kai don samar da makoma irin ta zamani ga Sin da Afirka.”
A gun taron, shugaban CMG, Shen Haixiong ya gabatar da rubutaccen jawabi, inda ya bayyana cewa, bai kamata matasan Sin da Afirka su shiga cikin harkokin shugabancin duniya kawai ba,matasa na da muhimmanci matuka wajen tsara tsarin shugabancin duniya. Ya kara da cewa, a ko da yaushe, CMG yana mayar da hankali kan hada kan matasan duniya, kuma yana goyon bayansu. Ya kara yin bayani cewa, ta hanyar amfani da harsuna 85 don watsa shirye-shirye ga kasashen duniya, CMG zai gina karin dandamali don tattara ra’ayoyi da tattaunawa, da ba da labarin matasa daga kasashe daban-daban game da yadda suke aiki tare, ta yadda za a taimakawa matasan duniya su inganta fahimtar juna ta hanyar musayar ra’ayoyi, da cimma matsaya daya ta hanyar cudanyar ra’ayoyi, da gabatar da damarmakin ci gaba, da kuma kirkirar makoma mai kyau tare. (Safiyah Ma)














