A yayin da duniya ke kara karkata ga amfani da nau’o’in makamashi marasa gurbata yanayi, kamfanoni da dama na kasar Sin suna ta kara shigewa gaba a fannin ingiza ci gaban fasahohin kirkire-kirkire.
Ga misali, kamfanonin kera ababen hawa na kasar Sin suna ta kara shiga sabbin matakan fadada ayyuka da gudanar da kirkire-kirkire, inda baya ga samar da hajoji masu saukin kudi da inganci, kamfanonin na Sin na kuma kara shigewa gaba a fannin jagorancin fasahohin zamani. Tabbas irin wadannan ci gaba na fasahohi, da kirkire-kirkire, ba kawai na haifar da sauyi a matsayin kamfanonin a cikin gida ba ne, har ma da tasirinsu a tsakanin sassan kasa da kasa, kasancewar gudunmawar da suka bayarwa ta kunshi tallafawa wajen cimma nasarorin yaki da sauyin yanayi.
A yanzu haka, kamfanonin kirar motoci masu amfani da lantarki na Sin na kara bunkasa fasahohinsu na batura masu inganci, da saurin caji, da na’urori masu aiki da fasahohin zamani irinsu kirkirarriyar basira ko AI, don kyautatawa, da saukaka tuki da nishadantar da masu amfani da su.
Alal hakika, wadannan ci gaba, ba wai haka kawai suka samu ba, tasiri ne na aiki tukuru na tsawon shekaru da kamfanonin suka yi, inda suka yi ta zuba jari, da fadada bincike a fannonin amfani da makamashi marar gurbata muhalli yadda ya kamata.
Wasu alkaluma sun nuna yadda daga shekarar 2016 zuwa 2022, adadin fasahohi masu nasaba da kere-keren na’urori masu fitar da karancin hayakin carbon na kasar Sin da aka yiwa rajistar ikon mallakar fasaha ya kai kaso 36.8 bisa dari cikin jimillar na duniya baki daya, kana wannan adadi na samun matsakaicin ci gaban kaso 9.3 bisa dari a duk shekara, duk da koma bayan da wasu kasashen duniya suka samu a fannin cikin wa’adin.
Da wadannan shaidu na zahiri, muna iya cewa himmar kamfanonin kasar Sin ta fuskar kirkire-kirkiren fasahohi, ya sanya hajojin kasar zama masu tafiya da yanayin zamani, wanda har kullum ake ta kokarin daidaita ci gabansa da bangaren kare muhalli, da aiwatar da matakai na inganta yanayin duniya.
Tun daga yankin kudu maso gabashin Asiya zuwa Turai, daga Latin Amurka zuwa gabas ta tsakiya har Afirka, ana ta ganin karuwar ababen hawa masu aiki da lantarki kirar kasar Sin, a wani yanayin dake shaida kwarewar kamfanonin kasar a fannin kirkire-kirkire fasahohi na zamani, wanda daga karshe ke dacewa da samar da hajoji irin wadanda kasuwannin duniya ke alfahari da kuma bukatar su. (Saminu Alhassan)














