Jakadan kasar Sin a Japan Wu Jianghao, ya gana da mataimakin ministan harkokin wajen Japan Takehiro Funakoshi a jiya Juma’a, inda ya bayyana matukar adawar kasarsa, da korafi a hukumance, dangane da kalamai marasa dacewa da firaministar Japan Sanea Takaichi ta furta dangane da kasar Sin.
Jakada Wu, ya ce munanan kalamai masu tayar da husuma na Takaichi, dangane da yankin Taiwan na Sin, wadanda aka jiyota tana yi kwanan baya, a majalissar dokokin kasarta sun sabawa hankali, sun tsallaka jan-layin kasar Sin, kana barazanar nuna karfi ne da neman takalar yaki. Kazalika, firaministar ta Japan ta ki amincewa da kuskurenta, ta ki janye kalaman, ko sassauta mummunan tasirinsu. Don haka matakin nata ya shaida matukar kaucewa gaskiya, da fankamar karfin da ba ta da shi.
Har ila yau, jakada Wu ya ce kalaman na Takaichi sun kasance matukar tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Sin, da keta dokar kasa da kasa, da ka’idojin cudanyar kasashen duniya, da manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da keta hurumin takardun siyasa hudu, wadanda Sin da Japan suka daddade, tare da matukar illata odar kasa da kasa bayan yakin duniya na 2, da tushen siyasa na dangantakar Sin da Japan.
Daga nan sai jakadan na Sin ya bayyana matukar bacin rai, da kin amincewar kasar Sin da hakan, da kuma mika kakkarfan sakon korafi, da adawa da matsayar firaminista Takaichi. (Saminu Alhassan)














