Babban jirgin ruwan yaki mai dakon sojojin kasa da sauran kayan yaki da ake amfani da su a kan-tudu samfurin 076 irinsa na farko a kasar Sin mai suna Sichuan, ya koma tashar jiragen ruwa da ke birnin Shanghai da misalin karfe 5 na yamma a yau Lahadi, bayan kammala gwajinsa na farko a teku.
Gwajin jirgin na kwanaki uku ya kunshi gwada ayyukan na’urar da ke sarrafa tafiyar jirgin da na’urorin lantarkinsa da sauran kayayyakin aiki, inda aka samu sakamakon da ake sa ran samu.
Kasancewarsa sabon jirgin ruwan yaki na zamani na rundunar sojojin ruwa ta ‘yantar da jama’ar kasar Sin, jirgin ya kunshi sabbin fasahohin majaujawar mayen karfe mai aiki da lantarki, da fasahohin rike jiragen sama bayan saukarsu, wadanda ke ba shi damar daukar jirage masu tsayin fukafuki, da jirage masu saukar ungulu da sauran kayan yaki masu aiki a cikin ruwa da kuma doron kasa. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)














