Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da harin da aka kai a Makarantar Sakandare ta ‘Yan Mata ta Gwamnati, Maga, a Jihar Kebbi, inda ya bayyana harin a matsayin mummunan halin rashin tsaron da kasar ke ciki.
Atiku, a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, ya ce ya yi matukar bakin ciki da lamarin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Mataimakin Shugaban Makarantar, sannan ya kai ga sace dalibai mata da dama.
A cewarsa, “Na yi matukar bakin ciki da labarin harin da aka kai a Makarantar Sakandare ta ‘Yan Mata ta Gwamnati, Maga, a Jihar Kebbi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Mataimakin Shugaban Makarantar, sannan ya kai ga sace daliban da ba su ji ba ba su gani ba. Wannan wani abin tunatarwa ne game da tabarbarewar rashin tsaron da ke faruwa a kasarmu.”
Ya kuma yi Allah wadai da kisan wani jigo na Jam’iyyar APC, Umar Moriki, da kuma sace-sacen jama’a da aka yi a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, inda aka sace iyalai baki daya, ciki har da mata da yara.














