Kimanin jarirai 8,933 ne aka haifa cikin mako daya a kasar Saudiyya, inji wani rahoto da Ma’aikatar lafiyar Kasar ta fitar.
Nazarin alkaluman an yi shine daga ranar 23 zuwa 30 ga Watan Augustan wannan shekarar.
Birnin Riyadh ne a kan gaba na yawan jarirai da aka haifa, inda birnin ke da sabbin haihuwa 2,286, sai Makkah inda ake da jarirai 1,804, inda gabashin kasar ke da 868.
Alkaluman sun nuna cewa yankin Najran na da jarirai sabbin haihuwa 249, sai yankin Asir mai 586 da Hafr Al-Batin mai 205 da yankin Hail mai 192 da Jazan mai 466 sai kuma birnin Tabuk da ke 291 inda birnin Bisha kuma ke da jarirai sabbin haihuwa 124.
A birnin Madinah kuwa an samu sabbin haihuwa 636, yayin da ake da 511 a Qassim da kuma 104 birnin Al-Qurayat.
A yankin arewacin kasar kuma, jarirai 166 aka haifa yayin da a Al-Jouf ake da 185 sai biranen Al-Baha da Al-Ahsa da ke da jarirai 109 da 351.