Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta cimma yarjejeniya da Graham Potter domin ya maye gurbin Thomas Tuchel da kungiyar ta kora a jiya Laraba.
A safiyar Talata ne dai shugaban kungiyar ta Chelsea, Todd Boehly, ya kori Tuchel, bayan tattaunawar da sukayi.
- PDP Ta Nada Sabon Shugaban Kwamitin Amintattu
- Hajjin 2022: Gwamnatin Zamfara Ta Mayar Wa Alhazai 1,318 Naira 50,000 Kowanne
Chelsea dai tayi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Dynamo Zagreb, a wasan da ta buga ranar Talata a gasar zakarun turai.
Tuni dai Graham Potter, wanda shine mai koyar da kungiyar Brighton Albion ya amince da kwantaragi mai tsawo da Chelsea kuma zai zama sabon mai koyar da kungiyar.
Potter, mai shekara 47 a duniya, a baya ya taba koyar da kungiyar Swansea City kuma an danganta shi da kungiyoyi da dama a Ingila.
Chelsea zata biya kungiyar Brighton fam miliyan 20 bayan da Brighton din wadda take mataki na 4 a teburin firimiyar Ingila ta amince ya tattauna da Chelsea.
Tuchel, dan asalin kasar Jamus ya lashe kofuna uku a Chelsea cikin watanni 20 da yayi a kungiyar ciki har da kofin zakarun turai na Champions league.
Chelsea tana mataki na 6 akan teburin firimiyar Ingila da maki 10 bayan buga wasanni shida kuma zata buga wasa na gaba da Fulham a ranar Asabar.