Fili na musamman domin matasa, wanda ya ke bawa kowa damar fadar irin namiji ko macen da yake so, tare da irin shagalin bikin auren da ake so, da kuma rayuwar zaman auren da ake so. A yau ma filin na tafe da wasu daga cikin sakonnin masu karatu kamar haka:
‘Namiji Dogo Fari Mai Kwantaccen Gashin Kai Nake So’
Ina son dogon namiji, fari, me kwantaccen gashin kai, mara kule-kule, mara girman kai, dan gayu. Irin auren da nake son mu yi irin wanda ake yi na kwana 1 ayi komai amma cikin awanni kowanne za a fitar masa da lokacin farawa da lokacin gamawa, za a kawata wajen yayi kyau da kyale-kyale, da fitulu, hatta kunshi ma a ranar za a yi, shagalin bikin dai zai kasance shi ba na indiya ba, kuma bana larabawa ba, kuma bana hausawa ba zai kamanceceniya duk da hakan, kuma a kaini a ranar komai dai ya zamo an yi shi a ranar.
Irin rayuwar zaman auren da nake so muyi irin wanda zamu kasance tamkar saurayi da budurwa wanda za mu ci gaba dda gudanar da duniyar soyayyarmu babu gundura.
Daga Suwaiba Sani Jihar Kaduna.
‘Ni Dai Na Zabi Mace Mai Kirki Da Mutunci’
Ina son auran mace me kirki me kima, me mutunci, bana son auren mace ‘yar Tiktok, irin wadanda za ki ga suna rawa a Tiktok gaskiya bana son mace me haka sabida na san indai tana yi ba za ta daina ba ya shiga jikinta, in ta haifa min yara za su tashi da rawar Tiktok.
Ina son shagalin bikinmu ya kasance kamar na zamanin baya, irin wanda ko kamu za a yi wa amarya tana rufe a cikin daki da kawayenta irin wanda ake yi tun muna yara, kuma za a kai amarya ranar da aka daura aure wato juma’a, sabida mu samu albarkar ranar.
Zaman auren da nake son mu yi , shi ne irin wanda kullum da safe za ta tashi ta gaishe ni bayan tayi sallah, sannan ta rinka goge mun takalmi, ta rinka rawar jiki da ta jiyo muryata, a takaice dai zaman biyayya.
Dan Ustaz Hafiz Jihar Katsina
‘Namiji Mai Fahimta Ba Mara Jin Magana Ba Na Zaba’
Ina son namiji me fahimta, ba irin namijin da ba a fada masa magana ya ji ba, ina son namijin da komai zan fada masa zai tsaya ya fahimce ni, bana son namiji baudadde, kuma kafaffe wanda in ya kafe a abu ya kafe kenan, bana son namiji irin wannan komai kudinsa bana sonsa.
Ina aure shagalin auren mu ya kasance irin na zamani wanda ake yayi, a kira Dj ya sha kida na lokaci daya ne, a jera kwana uku ana yi. Rayuwar auren da za mu yi ya zamo cikin lumana da kwanciyar hankali.
Daga Zainab Dahir Sokoto
‘Miji Baki Mai Dogon Hanci Ne Muradina’
Ina son namiji Baki amma ba sosai ba, kyakkyawa amma ba sosai ba, me hanci dogo, me ‘Yar karamar fuska ba sosai ba, bana son namiji kazami, wanda sai zai fita zai wanka.
Irin shagalin bikin da nake son a yi mana wanda za a rakashe, a girgije, a cashe inda hali ma ayi sati guda ana shagain biki. Rayuwar zaman auren mu ya zamo ko aiki zan yi ya rinka tayani, komai mu yi shi cikin soyayya.
Daga Habibah Naseer Usman Jihar Kebbi.