Yang Ning ta kasance ’yar asalin Jiangmen, wani kauye dake jihar Guangdi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta a kudancin kasar Sin.
A shekarar 2010, bayan ta kammala jami’a a Nanning, babban birnin jihar Guangdi, inda ta karanta fannin tafiyar da harkokin kasuwanci, ta koma kauyen Jiangmen domin aiki a matsayin jami’ar kauye.
- Ina So Na San Siffofin Jinin Haila?
- Sin Da Rwanda Sun Tsawaita Yarjejeniyar Hadin Gwiwa A Fannin Kiwon Lafiya Na Tsawon Shekaru 5
A yanzu, Yang Ning ce daraktar kwamitin kauyen. Ta kuma sadaukar da kanta wajen raya mahaifarta tare da taimakawa wajen horar da matasan kauyen.
Yang Ning ta bayyana cewa, “na bar gida domin karatu ne a lokacin da nake shekaru 12, kuma na dawo gida bayan na kammala jami’a.
Idan aka kwatanta da sauran yankunan kasarmu, rayuwa a garinmu ta fi sauki da kuma ganin ainihin rayuwa.
Na fi kowa fahimtar cewa, kauyenmu na bukatar matasan da za su jagorance shi wajen samun kyautatuwar rayuwa”.
Akwai kusan iyalai 500 a kauyen Jiangmen. Mazaunansa sun shafe gomman shekaru suna zaune cikin talauci.
A shekarar 2010, kowane mutumin kauyen na samun kimanin kudin Sin yuan 1000, kwatankwacin dala 153 ne a shekara.
“Na ga yadda wasu birane ke samun ci gaba cikin sauri. Bayan na dawo garinmu, ban ji dadin ganin talauci da koma bayan da ake fama da su ba. A wannan lokaci, na yanke shawarar sauya yanayin da taimakawa mazauna fatattakar talauci da kyautata rayuwarsu,” cewar Yang.
Nan da nan Yang ta fahimci cewa, aiki a kauyen ya bambanta da abun da ta yi tunani.
A wani lokaci, akwai abubuwan yi da yawa, da ba ta san ta inda za ta fara ba.
Ta kuma gane cewa, babu wata gajeriyar hanya da za ta bi, don haka dole ne ta yi hakuri ta ci gaba da nazari da koyo ta hanyar gwada abubuwa.
Wata rana, Yang ta taimakawa wani dattijon da bai iya karatu ba cike fom, domin ya nemi kudin gudanar da harkokin yau da kullum da gwamnatin kasar Sin ke bayarwa.
A washegari da ta isa ofis, bayan ta gama aiki a kauyen, sai Yang ta ga wani dattijo zaune a gaban ofishinta.
Ya ba Yang lemu, domin gode mata bisa taimaka masa da ta yi wajen cike fom din. Yang ta ce, “wani dan abu kadan na yi masa, amma ya taimaka masa sosai da iyalinsa.
Ya sa na ji cewa, aikina yana da ma’ana. Mutanen kauyen na da kirki, kuma ina son taimaka musu.”
Yang ta yi iyakar kokarin taimakawa mutanen kauyen shawo kan matsalolinsu. Pan Jiankiang, wani dattijo ne da yake kwance saboda rashin lafiya.
Yang ta kan kai masa magani akai-akai, kana ta taimaka masa samun tallafin kudi daga gidauniyar Tencent.
A wani lokaci ma, Yang ta taba taimakawa wata yarinya da iyayenta matalauta ne, na tsawon shekaru 6 domin ta samu damar kammala karatu.
Yanzu yarinyar da iyayenta na zama a gundumar, kuma rayuwarsu ta samu kyautatuwa. Domin taimakawa karin yara a kauyen, Yang ta kafa wani gida ga yaran da iyayensu suke aiki a birane. Tana amfani da lokacinta wajen wasanni da yaran.
A shekarar 2013, Yang ta shirya wani yawon shakatawa a lokacin rani, inda ta gayyaci daliban jami’a su raka yaran.
“Yang ta kan gudanar da ayyukanta bisa tsari,” cewar Jia Lidian, mataimakiyar darakta a kwamitin kauyen, kuma shugabar kungiyar mata ta Jiangmen. Lalubo hanyar fitar da mutane daga kangin talauci, daya ne daga cikin manyan burikan Yang.
“Ya kamata mu yi cikakken amfani da albarkatun dake akwai a Jiangmen, kuma mu raya muhallin shuke-shuke,” cewar Yang.
Bisa la’akari da dimbin albarkatun gora da wurin ke da shi, Jiangmen na wani wurin da ya dace da raya aikin sarrafa gora.
A 2021, bayan gudanar da nazarin kasuwa, Yang ta gamsu cewa sayar da kayayyakin gora da aka sarrafa kai tsaye ga masu saye a lardin Guangdong da jihar Guangdi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta, zai taimakawa mutanen kauyen samun karin kudin shiga.
Don haka, ta tuntubi masu saye, ta kuma taimakawa mutanen rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da musu sayen.
A sakamakon haka, manoman gora da masu sarrafa shi a kauyen, sun samu karin kudin shiga.
A 2014, mutanen kauyen da dama suka fara noman tattasai, amma mamakon ruwan sama da aka yi a shekarar, ya sa tattasan rubewa.
A shekara mai zuwa kuma, Yang ta jagoranci iyalai 90 wajen shuka saiwar Kudzubine.
Yang ta tuna cewa, “ba abu ne mai sauki jagorantar mutanen kauyen samun sa’a da yaki da fatara ba”.
Ta kuma karfafawa mutanen rungumar dabarun noma na gargajiya na kabilar Miao, domin noman shinkafa a muhalli mai dacewa da kuma daina amfani da maganin kashe kwari da takin zamani.
Wasu sun yi shakkun samun amfanin gona idan suka yi amfani da dabarun gargajiya. Amma domin kawar da shakkun, sai Yang da sauran wasu mutanen kauyen suka jagoranci noma na gwaji.
A kuma lokacin kaka, sun samu girbi mai armashi, kana sun sayar da shinkafan kan farashi mai rahusa. Daga nan, karin mutane suka bi dabarun Yang na noman shinkafa da kayan marmari da na lambu.
Haka kuma, Yang ta kaddamar da wani shirin karawa juna sani na yaki da talauci, ta hanyar sarrafa amfanin gona a kauyen, kuma kayayyakin na samun kasuwa sosai. Irin rikon gaskiya na Yang, ya sa mazauna kauyen suka aminta da ita.
Yang Meiyang, wata kurma, ta bayyana ta hanyar magana da hannu cewa, “a shirye nake in yi duk abun da Yang ta ce in yi.”
A 2016, Yang Ning ta kammala wa’adinta na biyu a matsayin jami’ar kauyen Jiangmen. “Yang na da kirki, kuma dukkanmu na sonta. Muna fatan za ta ci gaba da zama a kauyen.
Amma mun fahimci za ta fi samun ci gaba a babban birnin,” cewar wani mazaunin kauyen.
Haka ma wata abokiyar karatunta, ta yi kokarin shawo kanta don ta yi aiki a birni. Sai dai, Yang ta zabi ta zauna, ta kuma ci gaba da aiki a Jiangmen.
Ta ce, “ina jin na yi sa’ar rayuwa a wannan zamani, kuma a ganina, girmamawa ce shiga cikin gagarumin aikin yaki da talauci. Ba za a taba fahimtar yadda nake alfahari da zabi mai kyau da na yi, da abun da nake aiwatarwa ba.
Ana bukatar matasan da suke da basira da dabaru a yankunan karkara.” Yang ba ta taba daina laluben hanyoyin samar da karin kudin shiga ga mutanen kauyen ba.
Bisa aminta da suka yi da ita, an sake zabar Yang a matsayin daraktar kwamitin kauyen a 2017. Ita ce mace ta farko da ta kammala jami’a, da ta zama daraktar kwamitin kauye a gundumar Rongshui da take ciki.
An kuma zabe ta matsayin mataimakiyar wakilin jama’a na gundumar a wannan shekara. Kankanar da ake nomawa a kauyen na da zaki, kuma ana sayen su sosai. Yang ta taimakawa matan kauyen kafa wata kungiyar hadin gwiwa.
A watan Agustan 2018, kungiyar mata ta Rongshui ta shirya wani bikin girbin kankana a kauyen Jiangmen. “kankanarmu na da inganci sosai kuma suna samun karbuwa sosai a kasuwa.
Yang na da kwarewa, muna alfahari da farin ciki,” cewar daya daga cikin matan, yayin bikin. A shekarar 2020, Yang ta mika kudurin gyaran babban titin kauyen.
A watan Junairun 2021 kuma, aka gyara titin, karkashin goyon bayan gwamnatin karamar hukumar.
“A baya, sai mun dauki taki a bayanmu ko kafada mun hau tsaunika, inda muke noman kankana. Yanzu kuwa, muna iya zuwa a mota, cikin sauki muke sufurin taki da kankana.
Mun fi samun sauki a yanzu fiye da da,” cewar Zhang Haihui, wata mutuniyar kauyen.
An kuma kafa fitilu a kan titin, masu amfani da hasken rana guda 237.
“A 2020, mun karfafawa wasu mutane gwiwar noman wani nau’in laimar kwado, kuma sun samu girbi mai armashi.
A shekarar 2021, karin mutane suka shiga cikin noman, don haka sai muka fadada shirin na noman laimar kwado,” cewar Yang Ning.
Dong Yanfang, wata ‘yar kauyen ta furta cewa, “da karfafawar Yang, na noma laimar kwado a shekarar 2020, kuma na samu dubban kudade a shekarar. Na fara nomansa ne a bara.”
Wasu nau’ikan laimar kwado da ake ci, abubuwa ne na musammam da ake nomansu a yankunan kabilar Miao.
A baya, mutane da dama na jan kafa wajen noman wadannan abubuwa, saboda wahalar sayar da su. A 2016, Yang ta yanke shawarar sayar da kayayyakin amfanin gona domin tallata al’adu da cimaka masu dadi na kabilar Miao, ta kafar intanet.
Yang, tare da wasu jami’ai 6, sun kafa wata cibiyar sayar da amfanin gona ta intanet, kuma suka bude shafi a manhajar Wechat, ta yadda za su rika tafiyar da kasuwanci ta intanet. Sai suka fara sayar da kunshin cimaka ta intanet.
Daga sannan kuma, matasan kauyen da dama suka koma Jiangmen daga birane, domin aiki a cibiyar.
A 2020, saboda kokarin Yang da mutanen kauyen, Jiangmen ya fita daga kangin talauci.
Yanzu, masana’antu da dama na gudanar da ayyukansu a kauyen, kuma ababen more rayuwa a kauyen, da muhalli da yanayin zamantakewar jama’a, duk sun kyautatu matuka.
“Manufofin JKS da jami’an jam’iyyar ne suka haifar da kyautatuwar rayuwar mutanen kauyen,” cewar wasu mutane a kauyen.
A watan Nuwamban 2020, aka zabi Yang matsayin sakatariyar reshen jam’iyya na kauyen. Yang ta samu lambobin yabo da na karramawa da dama saboda gudummuwarta ga ci gaban yankin karkara a kasar Sin.
Daga cikinsu akwai na Mace mafi jajircewa ta duk fadin kasar Sin, da na yaki da talauci, da na matasa mafiya nagarta na kasar.
Haka kuma, Yang wakiliya ce ta majalisar mata ta kasa karo na 12. “Burina shi ne, hidimtawa mutanen kauyen, kuma shi ne ma’anar rayuwata.
]Ina fatan karin matasa za su bayar da gudunmuwar kuruciya da karfinsu, wajen farfado da yankunan karkara,” cewar Yang Ning.