• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

INEC Ta Dakile Yunkurin Kutse Cikin Rumbun Adana Bayananta – Farfesa Yakubu

by Sulaiman
3 years ago
Farfesa Yakubu

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa sababbin dabarun killace alƙaluman zaɓe ta hanyar na’urori da manhaja sun tabbatar da cewa zamanin sauya sakamakon zaɓe ko yin kutse cikin rumbun tattara bayanai ya wuce.

Yakubu ya bayyana haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki kan harkokin zaɓe da ƙungiyar YIAGA Africa ta shirya a Abuja.

  • 2023: Za A Bai Wa ‘Yan Hijira Damar Kaɗa Kuri’a A Sansanoninsu – INEC

Ya ce ko a zaɓen gwamna na jihohin Ekiti da Osun da aka yi a baya-bayan nan, ‘yan kutse daga ƙasashe daban-daban, har da wasu daga nahiyar Asiya, sun yi ƙoƙarin kutsawa rumbun tattara bayanai na INEC ta cikin manhaja domin su baddala alƙaluman zaɓen, amma ba su yi nasara ba.

Ya ƙara jan kunnen ma’aikatan hukumar da masu sa-ido cewa tilas sai an ƙara sa ido sosai kuma an ƙara ƙarfafa hanyoyin hana ‘yan kutse shiga manhaja domin baddala sakamakon zaɓe.

Farfesa Yakubu

LABARAI MASU NASABA

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

Ya ce: “Kuma mun ƙara jaddadawa da ƙara ɗora nauyin kulawa ga injiniyoyin mu cewa kada su yi sanyin jiki wajen hana duk wata ƙofar da ‘yan kutse za su iya kai farmaki a manhajar tattara sakamakon zaɓe.

“Waɗannan hanyoyi biyu da mu ka shigo da su yanzu su na da ingancin da babu yadda masu baddala sakamakon zaɓe ko masu kutse za su iya yin nasarar shiga rumbun tattara bayanai ko manhajar alƙaluman zaɓe.

“Hanyoyin biyu, wato tsarin amfani da na’urar BVAS da kuma manhajar IReV, su na da ingancin killace dukkan bayanai da alƙaluman zaɓe ba tare da shakkun an kutsa an baddala su ba.

Farfesa Yakubu

“Ita na’urar BVAS aikin ta shi ne tura hoton tambarin yatsan mai dangwala ƙuri’a da kuma tantance fuskar wanda ya dangwala yatsa bisa na’urar, sannan kuma ta kwafi fom na sakamakon zaɓe (EC8A) ta tura cikin manhajar IReV.”

A nasa jawabin, Babban Daraktan YIAGA Africa, Mista Samson Itodo,

Farfesa Yakubu

ya yi kira ga INEC da ta ƙara wayar wa da jami’an ta da waɗanda za a ɗauka aikin zaɓe nan gaba kai sosai domin su ƙara fahimta tare da samun ƙwarewa a dukkan hanyoyin da za a bi domin tattarawa, turawa da killace sakamakon zaɓe sun gudana a sauƙaƙe.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

NAWIA
Labarai

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

October 16, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

October 16, 2025
Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara
Labarai

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025
Next Post
An Kaddamar Da Yarjejeniyar Samar Da Nagartaccen Mulki A Arewa

An Kaddamar Da Yarjejeniyar Samar Da Nagartaccen Mulki A Arewa

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
NAWIA

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

October 16, 2025
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

October 16, 2025
Gaza

Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar?

October 16, 2025
Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

October 16, 2025
Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

October 16, 2025
Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

October 16, 2025
Tinubu

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

October 16, 2025
Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

October 16, 2025
Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.