Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Li Zhanshu, ya kai ziyarar nuna fatan alheri a kasar Rasha daga ranar Laraba zuwa jiya Asabar, bisa gayyatar da shugaban majalisar dokokin kasar da ake kira Duma, Vyacheslav Volodin ya yi masa.
A yayin ziyarar tasa, Li ya samu ganawa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Vladivostok da ke gabashin kasar, inda ya kuma tattauna da Volodin, da kakakin majalisar tarayyar Rasha Valentina Matviyenko a birnin Moscow, daga bisani kuma, ya gana da shugabannin bangarorin majalisar Duma ta biyar.
Yayin ganawarsa da shugaban Putin na Rasha kuwa, Li ya mikawa Putin din sakon gaisuwa da fatan alheri daga takwaransa na kasar Sin Xi Jinping.
Yana mai cewa, karkashin jagorancin shugabannin biyu, bisa manyan tsare-tsare da kuma kokarinsu na kashin kai, hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu wato Sin da Rasha bisa manyan tsare-tsare, a sabon zamani, yana ci gaba da bunkasa cikin sauri.
Shugaba Putin ya bukaci Li, da ya mika sakon fatan alheri ga shugaba Xi. Ya bayyana cewa, cikakken hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Rasha da Sin a sabon zamani, abu ne na musamman da kuma muhimmanci, kuma bangaren Rasha ya gamsu da huldar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma hadin gwiwar da yake yi da kasar Sin a fannoni daban daban.(Ibrahim)