Mutane shida da suka kunshi har da ‘yansanda uku da fararen hula uku ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai wa tawagar Sanatan da ke wakiltar mazabar Anambra ta Kudu, Sanata Ifeanyi Ubah.
Wasu ‘yan bindigan da ba a san ko su waye ba a ranar Lahadi sun farmaki tawagar Sanatan yankin Enugwu-Ukwu da ke karamar hukumar Njikoka a jihar Anambra.
LEADERSHIP ta labarto cewa hamshakin mai hada-hadar Mai wanda shine mamallakin kamfanin Capital Oil and Gas, yana kan hanyarsa ta dawo daga cocin Anglican Synod a Ozubulu da ke karamar hukumar Ekwusigo zuwa wani otel din da ke zaune a Awka ne ‘yan bindigan dauke da muggan makamai farmaki tawagar a daidai Enugwu-Ukwu.
Kamar yadda ganau suka shaida, harin ya wakana ne da karfe 5 na yammacin ranar Lahadi. An ce Sanatan ya tsallake rijiya da baya ne sakamakon yana cikin mota wacce harsashi baya iya ratsata.
“Ba za mu iya ce ga kalar wadanda suka kawo harin nan zuwa yanzu ba. Kuma babu wanda ya san dalilin kai harin, amma kila ya kasance domin siyasa ko don harkarsa ta kasuwanci, za a iya tunanin komai,” a cewar majiyar.
Kan wannan lamarin, cikin gaggawa gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya yi Allahwadai da harin tare da tabbatar da cewa wadanda suka kai farmakin ba za su sha haka nan ba dole sai sun dandana kudarsu kuma sai doka ta yi aiki a kansu.
Ya ce, wannan harin zai sanya su kawo karshen ayyukan ta’addanci a jihar.
Sakataren yada labarai na Soludo, Mr Christian Aburime, ya nakalto cewa gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga Sanata Ubah da kwamishinan ‘yansandan jihar CP Echeng Echeng, bisa rashin jami’ai da suka yi sakamakon harin.
Kazalika, daya daga cikin manyan masu kalubalantar kujerar Sanatan a zaben 2023, Kuma Dan takarar Sanatar mazabar na jam’iyyar APGA, Hon. Chris Emeka Azubuogu, ya yi tir da harin da aka kai wa Ubah ya nuna kwarin guiwarsa na cewa gwamnan Jihar ba zai yi sako-sako da wannan lamarin ba har sai an hukunta masu hannu a lamarin.