An yi bikin kaddamar da mataki na 2 na aikin kafa fitilu masu amfani da hasken rana na ba da hannu ga motoci a birnin Abuja, hedkwatar kasar Najeriya jiya Talata 13 ga wata, wanda kasar Sin ta ba da gudummowar gudanarwa.
Jakadan kasar Sin a Najeriya Cui Jianchun, da babban sakatare a hukumar kula da babban birnin tarayyar Najeriya Abuja Adesola Olusade, da ma wasu jami’an Sin da Najeriya sun halarci bikin.
A yayin bikin, jakada Cui ya ce, aikin yana cikin matakai masu nasaba da manyan ayyuka 9 da aka sanar, a taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, kana wani muhimmin bangare ne cikin manyan tsare-tsaren hadin gwiwa a tsakanin Sin da Najeriya. Sa’an nan kuma, aikin alama ce ta dankon zumunci a tsakanin kasashen 2.
A nasa bangare, Adesola Olusade, ya jinjinawa kasar Sin, bisa taimakon da ta dade tana bayarwa.
Ya ce aikin zai sassauta matsin lambar da ake fuskanta a Abuja, da kyautata zirga-zirgar birnin, da rage yawan hadarurrukan mota, da kuma saukaka zaman rayuwar mazauna birnin sosai. (Tasallah Yuan)