Rundunar ‘Yansanda ta cafke tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bayelsa kuma dan takarar kujerar Sanatan Bayelsa ta tsakiya a zaben 2023 na jam’iyyar PDP, Hon. Friday Konbowei Benson, bisa zargin takardar bogi.
Benson, wadda tsohon sakataren Gwamnatin jihar ne, a lokacin zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP ya kayar da sanatan da ke kan a wannan kujerar na Sanatan mazabar Bayelsa ta tsakiya, Moses Cleopas da kuri’u 110.
Cleopas dai bai ji dadin zaben fitar da gwanin da ya kai ga kayar da shi ba, inda ya dauki matakin kai karar Benson a gaban babban kotun tarayya da ke Yenagoa inda ke zarginsa da gabatar da takardun bogi ga hukumar zabe ta kasa INEC.
LEADERSHIP ta gano cewa jami’an ‘yansanda masu aiki a ofishin Sufeto Janar na ‘yansandan Nijeriya a ranar Laraba sun yin dirar mikiya a Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa tare da cafke Benson.
An ce sun dauke shi zuwa sashin binciken manyan laifuka (SCID) da ke jihar inda za a dauki bayansa.
Kwamishinan ‘Yansandan Jihar, CP Ben Okolo ya tabbatar da cewa tawagar jami’ai daga ofishin IGP sun je jihar, sai dai ya ce bai da masaniya kan binciken da suke yi a jihar.
A lokacin da aka tuntubi Sanata Cleopas ta wayar tarho ya karyata cewa yana a hannu wajen ingiza ‘yansandan cafke abokin hamayyarsa.
“Rundunar ‘yansandan Nijeriya ba a karkashin ikona suke ba, don haka, ba ni ke da damar sanyasu su gudanar da aikin da ke gabansu. Suna gudanar da aikinsu ne,” ya ce.
Dangane da cewa ko korafin da ya shigar a kan Benson ne ya kai ga kama ma shi, sai ya ce yana da ikon rubuta korafin.