Shugabar kungiyar mata ta kauyen Airikebeixi na garin Zhanmin dake gundumar Shufu a yankin Kashgar na jihar Xinjiang ta kasar Sin, kana, dalibar da ta gama karatu a cibiyar horon fasahohin sana’a ta jihar, Zaynura Namatqari ta ba da jawabi yayin taro karo na 51 na ofishin kare hakkin bil Adama na MDD wato OHCHR a jiya, inda ta yi bayani kan yanayin karatu a cibiyar horon fasahohin sana’a, tare da watsi da jita-jitar dake shafar jihar Xinjiang ta kasar Sin.
Cikin jawabinta, Zaynura Namatqari ta bayyana cewa, a yayin da take karatu a cibiyar, ta koyi harshen Sinanci, da ilmin shari’a, da fasahohin sana’a, da kuma ilmin kawar da tsattauran ra’ayi.
Kuma, ita da abokan karatunta sun yi karatu da rayuwa a cibiyar cikin yanayi mai kyau, kana an kare hakkokinsu yadda ya kamata.
A matsayin dalibar da ta gama karatu daga cibiyar, ta sanar da cewa, ba a taba yi wa daliba mace ko guda fyade ba. Cikin taron, ta kuma gargadi masu yada jita-jita cewa, idan suka ci gaba da bata sunan dalibai mata cibiyar, za ta nemi kare halaltaccen hakkinsu ta hanyar doka domin kare mutuncinsu. (Mai Fassara: Maryam Yang)