Ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2022 ne, aka shirya wani gagarumin bikin murnar cika shekaru 25 da dawowar yankin Hong Kong karkashin ikon kasar Sin, kana bikin kama aikin jami’an sabuwar gwamnatin yankin, da aka shirya a cibiyar taron jama’a dake birnin.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya je yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, ta jirgin kasa mai saurin tafiya don halartar bikin cika shekaru 25 da dawowar Hong Kong karkashin ikon kasar Sin, da kuma bikin rantsar da gwamnati ta shida ta yankin,
Jama’a daga sassa daban-daban na rayuwa a Hong Kong ne, suka yiwa shugaba Xi maraba, yayin da ya isa tashar jiragen kasa mai saurin tafiya ta Hong Kong West Kowloon. A jawabin da ya gabatar a bikin maraba da zuwa, Xi Jinping ya bayyana cewa, ranar 1 ga watan Yuli na bana ne, aka cika shekaru 25 da dawowar Hong Kong kasar Sin, kuma al’ummar kasar Sin na kabilu daban daban sun yi murnar bikin tare da ’yan uwa na Hong Kong.
A baya yankin Hong Kong ya sha jure jarrabawa masu tsanani a mabambantan lokuta, tare da shawo kan kowane hadari da kalubale. Daga bisani, yankin musamman na Hong Kong ya sake farfadowa, kuma a yanzu yana nuna kuzari mai karfi.
Shaidu sun kara tabbatar da cewa, “Tsarin kasa daya, amma tsarin mulki iri biyu” na da karfi sosai, kuma tsari ne da zai iya tabbatar da samun wadata da zaman lafiya da kwnaciyar hankali mai dorewa a Hong Kong, da kuma kiyaye alheri da moriyar mazauna yankin Hong Kong. Kamar yadda wani karin maganar Sinanci ke cewa, “Idan mun dage da tafiya, za mu isa wurin da muke so.” Muddin muka tsaya tsayin daka kan manufar “kasa daya, amma tsarin mulki iri biyu”, ko shakka babu makomar Hong Kong za ta yi kyau, kuma tabbas yankin Hong Kong zai ba da babbar gudummawa wajen farfado da al’ummar Sinawa.
Bayan dawowar yankin Hong Kong karkashin ikon kasar Sin yau shekaru 25 da suka gabata, yankin ya samu ci gaba matuka. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi hangen nesa matuka kan bunkasuwar yankin don tabbatar da cewa, an samu ci gaba mai dorewa karkashin manufar “kasa daya, amma tsarin mulki iri biyu”. Kuma tun bayan dawowar yankunan Hong Kong da Macao karkashin ikon kasar Sin, wannan manufa ta samu amincewa daga bangarori daban-daban.
Wannan ya shaida cewa, ita ce hanya mafi dacewa wajen warware matsalolin da aka bari a yankunan biyu, kuma manufa ce mai kyau wajen raya yankunan biyu mai dorewa a cikin dogon lokaci.
Bisa goyon bayan kwamitin tsakiyar jam’iyyar JKS karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, jerin tsare-tsare sun baiwa yankin Hong Kong zarafi da ba a taba ganin irinsa a tarihi ba. Daga shawarar “ziri daya da hanya daya” da tsarin raya babban yankin Guangdong da Hong Kong da Macao da kuma baiwa yankin taimamako wajen yakar cutar COVID-19 kuma tsarin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14 ya baiwa yankin sabon matsayi.
Duk wadannan sun shaida cewa, ci gaban da aka samu karkashin wannan manufa, ta samu amincewa daga bangarori daban-daban, kazalika yankin na hanzarta shiga tsarin gudanar da harkokin kasa, abin da zai tabbatar da bunkasuwar babban yanki da kuma taimakawa juna bisa fifikonsu.
Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana, bisa tallafin gwamnatin tsakiya, yankin Hong Kong ya yi amfani da fifikonsa, wajen samun nasarori masu ma’ana a fannin muhimman bincike, da hazaka, da kuma ci gaba a fannin kirkire-kirkire da fasaha a shekarun baya-bayan nan.
A yayin ziyarar duba rukunin masana’antun kimiyya na Hong Kong, bisa rakiyar tsohuwar jagorar yankin musamman na Hong Kong Carrie Lam, shugaba Xi ya ce, kamata ya yi gwamnatin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, ta ba da cikakken muhimmanci kan rawar da sabbin fasahohi ke takawa, wajen ba da taimako da jagoranci ga ci gaban tattalin arziki.
A zantawarsa da masana ilimi, da masu bincike, da wakilan matasa na masana’antun kirkire-kirkire kuwa, Xi ya yi kira ga yankin Hong Kong, da ya kara yin hadin gwiwa da biranen dake babban yanki cikin babban yankin Guangdong-Hong Kong-Macao, da karfafa hadin gwiwar ci gaban kamfanoni, da jami’o’i, da cibiyoyin bincike, da kara zage damtse don daga matsayin yankin Guangdong-Hong Kong-Macao, zuwa wata cibiyar kimiya da fasahar kirkire-kirkire ta duniya.
Xi ya bayyana fatan cewa, za a ci gaba da raya al’adun kaunar kasa da Hong Kong, tare da ba da gudummawa sosai, don gina kasar Sin wajen zama jagorar kimiyya da fasaha ta duniya.
A ganawarsa da sabon jami’in farko na hukumar gudanarwar yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin (HKSAR) John Lee, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga babban jami’in gudanarwar da kuma tabbaci game da makomar yankin Hong Kong, haka kuma mahukuntan gwamnatin tsakiya, za su baiwa John Lee da sabuwar gwamnatin yankin musamman ta Hong Kong cikakken goyon bayan, wajen tafiyar da harkokin mulki bisa doka.
Alkalum kididdiga sun nuna cewa, tun daga shekarar 1997 zuwa yanzu, GDPn yankin Hong Kong na kasar Sin, ya ninka sau biyu, wato ya kai dalar Hong Kong triliyan 2.8 ko fiye. Yawan cinikin kaya a yankin ya karu da ninki fiye da biyu, wato ya kai dalar Hong Kong triliyan 10, wanda ya kai matsayi na shida a duniya.
Yawan mutanen da suka samu aikin yi, ya kai miliyan 3 da dubu 650, wanda ya karu da kashi 15 cikin dari, kana yawan kamfanonin dake da hedkwata ko suka bude rassansu a yankin Hong Kong, ya karu zuwa kimanin dubu 4, wanda ya karu da kashi 57 cikin dari.
Bisa jerin sunayen cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya da aka fitar a watan Maris na bana, yankin Hong Kong ya ci gaba da rike matsayi na uku a duniya kana na farko a nahiyar Asiya, wannan ya sake tabbatar da matsayinsa na zama a kan gaba a fannin hada-hadar kudi a duniya. Ban da wannan kuma, sabbin bayanai sun nuna cewa, yanayin cinikayya a yankin Hong Kong ya kyautatu, kana tattalin arzikin yankin yana bunkasa cikin sauri.
A kwanakin baya, cibiyar Fraser ta kasar Canada, ta sake bayyana yankin a matsayin mafi ‘yancin tattalin arziki a duniya a rahoton shekara ta 2022 dake bayyana kasashe da yankuna mafiya ‘yancin tattalin arziki a duniya.
A karshen shekarar 2021, yankin Hong Kong ya zama yanki mafi ingancin tattalin arziki a duniya cikin shekaru 26 a jere. Masana tattalin arzikin yankin Hong Kong sun yi nuni da cewa, yankin ya samu wadannan nasarori ne, bisa goyon bayan Sin da kuma aiwatar da manufar “kasa daya, amma tsarin mulki iri biyu”. Tun daga shekarar 1997 wato lokacin da yankin Hong Kong ya dawo karkashin ikon kasar Sin, yankin ya samu babban ci gaba a matsayin cibiyar hada-hadar kudi ta duniya.
Yayin bukukuwan cika shekaru 25 da dawowar yankin Hong Kong karkashin ikon kasar Sin, kafar talabijin ta Documentary da tashar rediyo ta The Greater Bay, na kafar yada labarai ta CGTN ta kasar Sin, sun fara watsa shirye-shiryensu a yankin.
Tashar rediyo ta The Greater Bay, ta watsa bukukuwan murnar kai tsaye, cikin harshen Cantonese na yankin, daga cibiyar taruka da nune-nune ta Hong Kong, ciki har da na kaddamar da sabuwar gwamnatin yankin.
Shirye-shirye da dama masu kayatarwa da aka gabatar kan maudu’ai daban-daban da aka watsa a ranar farko, sun ja hankalin mazauna yankin, inda bangarori daban-daban daga Hong Kong din da Macao, suka yi ta aikewa da sakon taya tashoshin murna.
Albarkacin wannan rana mai muhimmanci, an bude dakin adana kayan tarihi na fadar sarakuna ga al’umma a shiyyar al’adu ta West Kowloon, dake yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin. Sama da kayayyakin tarihi 900 da aka nuna, an samo su ne daga fadar sarakuna wato Palace Museum dake Beijing, kuma wasu daga cikinsu an nuna su ne a Hong Kong a karon farko.
Rahotanni na cewa, an sayar da kusan kashi 80 cikin kashi 100 na dukkan tikitoci 140,000 na shiga dakin adana kayan tarihin cikin makonni hudun farko da budewarsa.
Kevin Yeung, sakataren hukumar raya al’adu, wasanni, da yawon bude ido na gwamnatin yankin musamman ta Hong Kong na kasar Sin, ya ce dakin adana kayan tarihi na fadar sarakuna zai kara yin amfani da fifikon da yankin Hong Kong yake da shi ta fuskar al’adu, wajen bayyana kyakkyawan tarihin kasar Sin yadda ya kamata.
Ita ma Madam Peng Liyuan, mai dakin shugaban kasar Sin Xi Jinping ta ziyarci cibiyar wasannin kwaikwayo na gargajiyar kasar Sin, wadda ke yankin al’adun na West Kowloon, a yankin musamman na Hong Kong, don fahimtar yanayin wurin, da yadda yake samun ci gaba, har ma ta tattauna da ma’aikatan wurin.
A lokacin babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, shugaban kasar Xi Jinping ya nuna kulawa matuka game da wadata da zaman lafiyar yankin musamman na Hong Kong, da moriyar walwalar jama’ar wurin, inda ya yi nuni da cewa, ci gaba shi ne ginshikin raya yankin Hong Kong da kuma magance matsaloli daban-daban.
Tambaya a nan ita ce, shin ta yaya yankin Hong Kong zai samu sabon ci gaba cikin shekaru 5 masu zuwa?
A yayin bikin cika shekaru 25 da dawowar Hong Kong karkashin ikon kasar Sin, da kuma bikin rantsar da gwamnatin yankin ta shida, wanda aka gudanar, shugaba Xi Jinping ya gabatar da wasu dabaru 4 da yake fatan za su samar da ci gaban yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin.
Wadannan dabaru guda hudu sun hada da “Mayar da hankali kan kara matsayin shugabanci” da “Kara karfin inganta ci gaba” da “Warware matsalolin da jama’a ke fuskanta “, da kuma “Wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tare”.
Shugaba Xi ya kuma bayyana fatan sabuwar gwamnatin yankin, za ta aiwatar da manufar nan ta “kasa daya, mai tsarin mulki iri biyu” tare da gudanar da ayyuka masu amfani, da kuma mai da hankali kan warware batutuwan da suka fi damun mazauna yankin na Hong Kong.
Xi ya bayyana cike da kauna cewa: “A halin yanzu, abin da ya fi jan hankulan jama’ar Hong Kong shi ne, fatan samun rayuwa mai inganci, da zama a isasshen gida, da samun karin damammakin raya sana’o’i, da samar da ilimi mai inganci ga yara, da kuma samun kulawa mai inganci idan an tsufa.” Don haka, ya bukaci sabuwar gwamnatin yankin da ta dauki bukatar al’umma, musamman ma fararen hula, a matsayin babbar manufarta ta gudanar da mulki.
Bisa la’akari da yadda ake matukar bukatar tsaro don samun ci gaba, shugaba Xi Jinping ya ce, bayan fuskantar tashin hankali, kowa yana jin cewa, yankin Hong Kong ba zai kasance cikin rudani ba, kuma ba za a hanzarta ci gaban yankin ba. Yana mai cewa, wajibi ne a kawar da duk wata irin katsalandan tare da mai da hankali kan ci gabansa.
Yanzu dai yankin Hong Kong ya zabi shugabanni masu kishin kasa, wadanda suka fara aikin jan ragamar harkokin yankin tun daga ranar 1 ga watan Yulin wannan shekara. Matakin da masu sharhi ke cewa, an bude wani sabon babi a yankin, tun bayan da aka kafa sabbin dokokin tsaron kasa da na zabe masu alaka da yankin.
Burin kowace kasa mai ’yanci dake da kishin muhimman muradun al’ummominta, shi ne kare rayuka da dukiyoyin jama’a maimakon zangar-zangar da za ta kai ga koma bayan kasa da al’ummarta a dukkan fannoni, kuma kowa da irin kiwon da ya karbe shi.
Haka kuma, duk wata kasa mai cikakken ’yanci, wajibi ne tana da dokar tsaron kasarta. Kuma duk wanda ya karya doka, tilas ne doka za ta taka shi. Da ma “Icce aka ce, tun yana danye ake lankwasa shi”. (Ibrahim Yaya)