Jiya Alhamis ne aka gudanar da taron murnar cika shekaru 60, da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da kasar Uganda ta kafar bidiyo.
A yayin taron, mataimakin shugaban kungiyar sada zumunci da kasashen waje ta kasar Sin Jiang Jiang, ya bayyana cewa, a halin yanzu, ya kamata kasar Sin da kasashen Afirka su hada kansu, wajen karfafa hadin gwiwa a fannonin gina ababen more rayuwa, da gudanar da kirkire-kirkire ta fuskar harkokin sadarwa, da neman bunkasuwa ta hanyar kare muhalli, domin neman babban ci gaba.
- ’Yan Sama Jannati Na Kasar Sin Sun Gayyaci Matasan Duniya Da Su Ziyarci Tashar Sararin Samaniyar Sin
A nata bangare, jakadar kasar Uganda dake kasar Sin Oliver Wonekha ta bayyana cewa, shekarar 2022 wata muhimmiyar shekara ce, domin a cikin ta ake cika shekaru 60 da kafuwar huldar diflomasiyya a tsakanin kasar Uganda da kasar Sin, kuma cikin wadannan shekaru da suka gabata, ana ci gaba da zurfafa dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu, yayin da aka cimma sakamako da dama.
Tana mai cewa, “Kasar Sin ta kasance daya daga cikin kasashen da suka fi zuba jari a kasar Uganda, wanda hakan ta taka muhimmiyar rawa a fannin raya tattalin arzikin kasar Uganda, shi ya sa, gwamnatin kasar take godiya matuka dangane da taimakon da kasar Sin ta samar mata.
Kaza lika kasar Sin ta samar da taimakon kudi ga wasu muhimman shirye-shiryen raya kasar Uganda, kamar na gina tashar samar da wutar lantarki da karfin ruwa ta Karuma, da gina manyan hanyoyin mota tsakanin birnin Entebbe da birnin Kampala da sauransu.
Kuma, bisa bayanin da aka fidda, ya zuwa shekarar 2020, karfin cinikayya a tsakanin kasashen biyu, ya zarce dallar Amurka har biliyan 1.
Kasar Sin ta kuma ba da gudummawa matuka ga kasar Uganda, a fannin gudanar da kwaskwarima, da neman ci gaba, bisa tsarin dandalin tattauna hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC”. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)