Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya zanta da takwaransa na Amurka Antony Blinken a jiya Juma’a, a ofishin zaunanniyar tawagar Sin a MDD da ke birnin New York.
Yayin zantawar tasu, Wang Yi ya ce a yanzu haka, dangantakar Sin da Amurka na cikin wani yanayi mai cike da kalubale, kuma akwai darussa da ya dace Amurka ta koya daga hakan. Kaza lika kamata ya yi manyan kasashen biyu su gaggauta gina wata turba mafi dacewa, domin ingiza daidaiton alakar dake tsakanin su.
Wang Yi, ya kuma sake jaddada matsayar kasar Sin game da kurakuren da Amurka ta tafka, game da batun yankin Taiwan, yana mai cewa, ya wajaba Amurka ta komawa sanarwa 3 da ta sanya hannu kan su tare da Sin, da na manufar kasar Sin daya tak a duniya, ta kuma fayyace adawar ta karara, da ayyukan masu rajin “Samun ‘yancin kan Taiwan”.
A nasa bangare, Mr. Blinken ya ce, tabbas alakar Amurka da Sin na fuskantar mawuyacin yanayi, kuma mayar da alakar sassan biyu kan turba ta gari, zai yi matukar amfanar kasashen.
Ya ce a baya, Sin da Amurka sun yi nasarar warware banbance banbancen dake tsakanin su, kuma a yanzu ma Amurka a shirye take, ta gudanar da managartan shawarwari, da tattaunawa tare da Sin, domin kaucewa rashin fahimtar juna, da kuskuren manufa, ta yadda daga karshe za su cimma nasara tare.
Kaza lika Mr. Blinken ya jaddada cewa, Amurka ba ta da burin shiga wani sabon yanayi na cacar baka, kuma matsayin ta game da manufar kasar Sin daya tak a duniya bai sauya ba, kana Amurka ba ta goyon bayan samun ‘yancin kan yankin Taiwan “. (Saminu Alhassan)