Ginin wanda aka yi shi da duwatsu a kusa da gabar Kogin Thames, yana bangaren dama da ginin Majalisar Dokokin Birtaniya a tsakiyar birnin Landan, Cocin Westminster Abbey ya kasance wani wurin shirya kasaitattun bukukuwan kasa masu alfarma cikin karni masu yawa.
Cocin ta kasance mai dimbin tarihi, inda ake nada sarakunan Birtaniya ciki har da bikin nadin Sarauniya da aka yi a shekarar 1953.
Ginin wanda ake gani yanzu, an sake gina shi ne a zamanin Sarki Henry III, a 1245 to amma an gina ta ne tun a shekarar 960AD.
Dakta Hannah Boston, malama a Kwalejin Magdalen ta Jami’ar Odford ta ce ‘Ginin ya kasance wani wurin taron siyasa da mulkin Ingila na kusan dubban shekaru.
A yau fiye da fitattun mutane 3,300, wadanda suka hadar da sarakuna, sun kasasnec ko dai an binne su a ciki, ko kuma a shirya gawarwakinsu a cikin cocin Westminster Abbey.
A yayin da miliyoyin mutane ke bankwanan karshe da gawar Sarauniya Elizabeth II a lokacin jana’izarta daga Cocin ta Westminster Abbey, ga wasu abubuwa biyar game da tsohon ginin.
1. An daura auren iyalan gidan Sarauta 16 a cikinta
A shekarar 2011, sanye da tufafi masu launin ruwan dorawa Sarauniya Elizabeth II, ta halarci daurin auren jikanta Yarima William da matarsa Kate Middleton, wanda shi ne aure na baya-bayan nan da aka daura a cocin.
Daurin auren Yariman ya biyo bayan jerin auren gidan sarautar da ake yi a cocin tun shekara 900 da suka gabata.
Kawo yanzu an daura aure 16 na iyalan gidan sarauta a cocin, tun daga kan auren Henry I, wanda ya auri Gimbiyar Scotland Matilda a shekarar 1100, da kuma auren Elizabeth lokacin tana Gimbiya tare da mijinta Yarima Philip a shekarar 1947.
2. Gidan da tsohuwar kofar Birtaniya take
A shekarar 2005 wani bincike ya gano cewa a Cocin Westminster Abbey ne tsohuwar kofar masarautar Birtaniya take.
An kera kofar ne a shekarun 1050, gabanin yakin Norman.
Dakta Boston ta ce Sarki Edward wanda ya yi zamani tsakanin shekarun 1042 1066, shi ne ya gina cocin.
To amma cikin abubuwan da aka gina cocin da su tun wancan lokaci, zuwa yanzu kofar ce kawai ta rage.
3. Makabartar manyan sarakuna, da wasu dubban mutane
Cocin Westminster Abbey ta kasance makabarta ga Sarakunan Birtaniya kusan 30, na farko shi ne Sarki Edward. Sauran sun hada da Sarauniya Elizabeth I, da Sarauniyar Scots, da kuma gimbiyoyi 11 (matayen Sarakuna masu ci) Sarki na karshe da aka binne a cocin shi ne Sarki George II a shekarar 1760, to amma ba sarakuna kadai ake binnewa a cocin ba.
An binne fitattun mutane fiye da mutum 3,300 a cocin, wadanda suka hada da Sir Isaac Newton, da Stephen Hawking, da George Frederic Handel da kuma marubuciyar wakokin nan Mary Trebor.
A nan ne kuma aka binne shahararrun mawaka da marubuta, kamar su Jane Austen da Charlotte, da Emily da kuma Anne Brontë.
Jana’iza ta baya-bayan nan da aka yi a cocin ita ce jana’izar Gimbiya Diana a shekarar 1997, sai kuma ta Sarauniya Elizabeth II da aka yi a yanzu.
4. Kujerar nadin sarauta
Ana yi wa kujerar nadin sarauta kallon daya daga cikin manya kuma fitattun kujeru a fadin duniya, kuma ta kasance a cikin wannan gini tsawon karni bakwai.
Sarki Edward I ne ya kera kujerar daga wani fitaccen dutse mai dimbin tarihi da ya dauko daga yankin Scotland.
Sarauniya Elizabeth II ta zauna a kan kujera da aka ajiye kan dutsen yayin bikin nadinta a shekarar 1953, haka kuma za a sake fito da kujerar a yayin bikin nadin sabon sarki Charles lll.
Tun shekarar 1066, duka sarakunan da aka nada in ban da guda biyu an nada su ne a cocin Westminster Abbey, inda ka nada sarakuna 39.
5. Wurin tarihi ne na hukumar kula da al’adu da tarihi na Majalisar Dinkin Duniya, kuma wasu taswirar gine-ginensa na hasashen karshen duniya
An kawata gaban saman ginin cocin da jerin kananan gumaka masu ruwan zinari, wadanda suke uku daga cikinsu ke hasahen lokacin tashin duniya.
An gina su ne da wasu kanana-kananan duwatsu masu launin ruwan gilashi da ke dauke da launuka masu yawa, wadanda aka yanka zuwa suffofi daban-daban.
Gumakan wadanda ake kira da gumakan Cosmati, suna hasashen cewa duniya za ta wanzu zuwa shekara 19,683.
A baya-bayan nan ne dai sakon da wadannan gumaka ke dauke da shi ya bayyana ga mutane, bayan da aka yi wa ginin cocin kwaskwarima inda aka kawar da wasu abubuwan da a baya suka rufe wannan sako.
A shekarar 1987 wadannan gumaka da tsohuwar kofa, tare da kujerar sarautar suka zama wasu abubuwa masu muhimmanci da al’adun duniya, a lokacin da aka lissafa fadar Westminster da cocin Westminster Abbey, cikin kayayyakin hukumar UNESCO.
Mun ciro muku daga BBC.